Barazanar Boko Haram: Ba zan mayar da martani ba yanzu- Pantami
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Dokta Isa Ali Pantami, ya shaida cewa zuwa yan zu ba zai ce ko mai ba game da barazanar da jagoran wani bangare na kungiyar Boko Haram Abubakar Shekaru ya yi masa ba. Shaikh Pantami, ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake gabatar da mukala akan fasahar zamani […]
Isa Ali Pantami, Ministan Sadarwan Najeriya. (Tsohuwar ajiya).
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Dokta Isa Ali Pantami, ya shaida cewa zuwa yan zu ba zai ce ko mai ba game da barazanar da jagoran wani bangare na kungiyar Boko Haram Abubakar Shekaru ya yi masa ba.
Shaikh Pantami, ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake gabatar da mukala akan fasahar zamani a makarantar sakandare ta Garki da ke birnin tarayya Abuja. Inda yake amsa tambayoyin manema labarai sai ya ce, “Babu abin da zance kan wannan barazanar a yanzu.”
Ministan na yin rangadi a makarantun sakandaren ne, inda yake yi wa dalibai lakcoci kasancewar da dama daga cikin su na fuskantar karancin wadanda zasu basu shawarwari akan fannin ilimin fasahar sadarwa da irin tasirin fannin ga tattalin arzikin kasa na zamani.
‘Yan ta’adda na amfani da shafukan zumunta don samun mambobi – Pantami