Barazanar Hukumar WAEC ga Jihohin Arewa
A karshen makon jiya ne Hukumar shirya jarrabawa ta yankin Afirka (WAEC) ta bayar da sananwar ba za ta saki jarrabawar da daliban Jihohin Arewa suka rubuta na watan Mayu da Yunin wannan shekara (2015) ba ganin yadda jihohin suka kasa biyan dimbin basussukan da hukumar ke binsu bashi.Mista Charles Eguridu, babban jami’in da ke […]
A karshen makon jiya ne Hukumar shirya jarrabawa ta yankin Afirka (WAEC) ta bayar da sananwar ba za ta saki jarrabawar da daliban Jihohin Arewa suka rubuta na watan Mayu da Yunin wannan shekara (2015) ba ganin yadda jihohin suka kasa biyan dimbin basussukan da hukumar ke binsu bashi.
Mista Charles Eguridu, babban jami’in da ke shugabantar ofishin hukumar da ke Najeriya ne ya sanar da haka. Ya ce saboda dimbin basussukan da hukumar ke bin wadansu jihohi ne ta sa hukumar ta fada cikin mawuyacin hali na rashin isassun kudi. Ya ce hukumar tana bin Jihohi 19 na Arewacin Najeriya basussukan da suka kai Naira biliyan 4 kawo yanzu.
“Hukumar shirya jarrabawa ta WAEC tana bin Jihohin Arewa basussukan jarrabawa na dalibansu. Da yawa ma daga cikinsu ba su biya hukumar basussukan da ake bin su na shekarar 2014 ba ballantana na wannan shekara (2015). Mun rubuta wasiku ga wadannan jihohi a kan batun, amma har yau ba mu ji amsa daga gare su ba. Yin haka kuma ba karamin matsala ce ga hukumar shirya jarrabawar ba. Don haka muna kira ga wadannan jihohi da su yi wa Allah su biya kudaden da hukumar take bin su bashi na rajistar dalibansu wanda suka rubuta jarrabawar WAEC. Don haka kada wani ko wasu su ce za su zargi hukumar idan ba ta saki sakamakon jarrabawar ga daliban jihohin da abin ya shafa ba”, inji shi.
Kwana daya da yin wannan bayani ne sai wadansu daga cikin iyayan daliban suka yi kira ga Gwamnatocin jihohin da kada su yi wasa da karatun ’ya’yansu don yin haka zai jefa su da kuma kasar nan cikin bala’i. Haka su ma ’yan majalisun wakilai na tarayya sun bayyana takaicinsu akan wannan batu. Sun ce muddin hukumar shirya jarrabawar (WAEC) ta rike sakamakon daliban da jihohin su ba su biya kudin jarrabawarba, to hakan zai jefa kasar nan da yankin Arewa da iyayen yaran da kuma su kansu daliban cikin mummunan hali. Don haka suka yi kira ga jihohin da abin ya shafa su yi kokarin biyan hukumar basussukan da take bin su.
Abin bakin ciki ne yadda wadansu jihohi suke yin alkawarin da suka san ba za su iya cikawa ba, musamman a bangaren biyan kudin jarrabawar sakandaren dalibai. Hukumar WAEC ma tana da laifi. Tun farko bai dace ta amince da alkawurran da gwamnatocin suka rika yi mata ba, inda ta bari sai da kudin suka yi yawa kafin ta fara daukar mataki. Babu inda aka nuna a dokar hukumar shirya jarrabawar ta (WAEC) dalibi zai iya rubuta jarrabawa a bashi ba. Yakamata a ce hukumar ta dage a kan dokarta na sai dalibi ko gwamnati ta biya kafin a bari kowane dalibi ya rubuta jarrabawa. Da hukumar ta dage a kan wannan tsari, ko shakka babu ba za ta tsinci kanta a cikin wannan hali ba. Ta sani wannan mataki da take shirin dauka na kin sakin jarrabawar daliban sakandaren da suka fito daga Jihohin Arewa zai kawo cikas ga Arewa da ma kasar nan baki daya. Hukumar ta dai yi kokarin bin hanyoyin da suka kamata don ganin jihohin sun biya ta basussukan da take binsu bashi. Sannan ta sani wannan ya zama darasi a gareta, kada ta sake amincewa da dadin bakin wani ko wasu wajen barin dalibai zama don su rubuta jarrabawar ba tare da sun biya, ko an biya musu ba. daya daga cikin hanyoyin da ya dace hukumar ta bi don ta kwato kudinta daga wadannan jihohi shi ne ta buga sunayen irin wadannan jihohi a jaridu da kafofin watsa labarai don duniya ta sani.
Sannan jihohin da abin ya shafa yakamata su gane cewa idan suka yi wasa da karatun dalibansu, hakan zai iya jefa jihohin cikin matsalolin da za a dade ba a shawo kanta ba. Da ma al’amarin karatu a Arewa sai a hankali ganin yadda Jihohin Kudu suka yi wa na Arewa nisa a harkar karatu. Iyaye su daina yin rikon sakainar kashi da karatun ’ya’yansu. Su sani alhakinsu ne su biya wa ’ya’yansu kudin karatu. Su daina bari wani ko wasu suna yin siyasa da batun karatun ’ya’yansu. A wannan zamani na siyasa ne za ka ji ’yan siyasa da gwamnatoci suna fadin sun dauke wa iyaye biyan kudin karatun yaransu alhali kuma ba zama tilas ba. A duk lokacin da aka ki cika irin alkawari, sai ka ga iyayen da kuma yaran sun shiga cikin matsala. Tambayar ita ce, ta yay jihohin da suka kasa biyan albashin ma’aikatansu na wata da watanni a ce su ne kuma za su iya biyan kudin jarrabawar daliban da tun farko bai rataya a wuyansu ba? Don haka jihohin da abin ya shafa su yi kokarin ganin sun biya basussukan da hukumar WAEC take bin su don a kauce wa matsalolin da za su iya haifarwa na jefa daliban da kuma hukumar cikin matsala. Su daina daukar alkawurran da suka san ba za su iya cikawa ba.