Barazanar kai mini hari ba za ta hana ni aiki ba – Kwamishina

Kwamishinan ‘Yan sanda a Jihar Kurosriba, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce ko kusa barazanar kai masa hari da wasu kungiyoyin asiri suka yi sakamakon hana su aikata miyagun laifuka, ba zai sa shi yin kasa a gwiwa ba, wajen aikinsa da kuma yaki da ‘yan ta’adda, domin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro […]

Barazanar kai mini hari ba za ta hana ni aiki ba – Kwamishina

Kwamishinan ‘Yansandan jihar Kuros riba Hafiz Muhammad Inuwa

Kwamishinan ‘Yan sanda a Jihar Kurosriba, Hafiz Muhammad Inuwa ya ce ko kusa barazanar kai masa hari da wasu kungiyoyin asiri suka yi sakamakon hana su aikata miyagun laifuka, ba zai sa shi yin kasa a gwiwa ba, wajen aikinsa da kuma yaki da ‘yan ta’adda, domin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a Jihar Kurosriba.

Kwamishinan ya bayyana haka ga wakilinmu a yayin wata tattaunawa a farkon wannan makon. Kwanakin baya ne wasu kungiyoyin asiri suka rabawa manema labarai takardun sanarwar cewa za su kai wa kwamishinan ‘yan sandan da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS na jihar, yana mai cewa “Akwai wannan barazana amma daidai da rana daya wannan ba zai sa inyi masu rangwame ba, akan haka nema na cewa jami’ai na mu kara zage damtse wajen ci gaba da kai wa wadannan kungiyoyi farmaki,” Inji shi.

Hakan kuma kwamishinan ya ce a yanzu haka sun kama masu laifi 59 da suka addabi jama’ar jihar da aikata miyagun laifuka. “Hukumar ‘yan sandan Jihar Kurosriba ta kama miyagun mutane da ake zarginsu da aikata laifuka daban-daban. 24 bisa laifin yin fashi da makami, inda muka kwace bindigogi 15, daga cikinsu akwai mutane 12 masu satar baturan fitilun kan titi.

“Akwai kuma biyu daga cikinsu da aka kama ake zarginsu da laifin kisan kai, sai kuma mutum biyar da zargin aikata fyade. Mutum shida ‘yan kungiyar asiri, sai kuma musu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa mutum takwas. An kuma kama wasu rukunin mutum uku da bindigogi da ke amfani da su wajen sata,” a cewarsa.

Daga nan ya gargadi duk wani mai aikata mugun hali ya tuba ya daina, domin ya ce hukumarsa ba za ta kasa yin aiki a kansu ba, sannan ya gargadi iyayen yara su rage kwadayin abin duniya, su kula da ‘ya’yansu saboda yawaitar samun karuwar yi wa kanana yara fyade, sannan ya nemi jama’a da su ci gaba da ba su bayanan sirri na maboyar miyagu domin su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kakkabe bata gari cikin al’umma.