Najeriya ta cafke bakin haure 33 a Ogun

Jami’an hukumar sun cafke mutanen ne a maboyarsu da ke yankin Karamar Hukumar Odeda ta Jihar Ogun, ba tare da takardun izinin shigowa Najeriya ko wata sana’a ba.

Najeriya ta cafke bakin haure 33 a Ogun

Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Kasa

Hukumar Shige da Fice ta cafke bakin haure 32 ’yan kasashen Chadi da Togo a Jihar Ogun.

Jami’an hukumar sun cafke mutanen ne a maboyarsu da ke yankin Karamar Hukumar Odeda ta Jihar Ogun, ba tare da takardun izinin shigowa Najeriya ko wata sana’a ba.

Da yake gabatar da su, kwamandan hukumar na jihar, Jibrin Yakubu ya ce bayyana mutanen a mastayin barazanar tsaro ga Najeriya kasancewa sun shigo ne ta barauiyar hanya kuma babu wanda ya san dalilin zuwansu.

Ya ce, “Mun samu rahoto ne daga mazauna garin Odeda game da zuwan wasu ’yan kasahen waje da ba sa jin wani yare sai Faransanci.

“Ranar Laraba da misalin karfe 12 na dare muka kai samame a wasu wurare inda muka maka mutum 33 muka kawo su babban ofishinmu.

“A yayin daukar bayanansu mun gano cewa 33 daga cikinsu ’yan kasar Chadi ne, sai muum daya daga kasar Togo.

“Da muka tambaye su dalilin zuwansu da kuma kasancewarsu ’yan kasa daya sai suka ce dan Togo din ne ya gayyato su zuwa taron kasuwanci.

“Sai da suka yi rajista kuma za su biya karin wasu kudaden, sannan duk mako za a tura musu kudade a asusun ajiyasu.

“Amma da muka nemi sanin harkar da shi dan Togo din yake yi, da har ya dauke su aiki, ya kasa nuna wani abu kwakkwara, shi ya sa muka yanke shawarar tattala wa daukacin al’ummar kasa domin kar su fada a tarko,” in ji shi.