Barcelona ta sawwaƙe wa Xavi Hernandez
Ana sa ran tsohon kocin Bayern Munich da Jamus, Hansi Flick ne zai maye gurbin Xavi.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernandez bayan kammala kakar wasan bana ba tare da lashe kofi ba.
Xavi zai bar Barcelona ne bayan wasan da ƙungiyar za ta yi da Sevilla a ranar Lahadi.
- ’Yan Boko Haram 119 Sun Mika Wuya Cikin wata 1 —MNJTF
- Yadda ake bikin mika wa Muhammadu Sanusi II takardar aiki
Sallamar Xavi da Barcelona ta yi na zuwa ƙasa da wata guda bayan ya sanar da aniyarsa ta ci gaba da zama a ƙungiyar biyo bayan raɗe-raɗin raba gari da ita ya riƙa yamutsa hazo.
Cikin wata sanarwa da Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya fitar a wannan Juma’ar, ya ce “ƙungiyar ba ta buƙatar aikin Xavi a kakar wasa ta gaba.”
Tun a karawar da Barcelona ta yi da Rayo Vallecano a ranar Lahadi, magoya bayan ƙungiyar suka soma kiraye-kirayen neman Laporta ya ƙyale Xavi ya ci gaba da zama a ƙungiyar.
Wannan kiraye-kiraye da magoya bayan ƙungiyar suka riƙa yi ya tabbatar ƙarara cewa Laporta ya shirya sawwaƙe wa Xavi daga aikin horas da ƙungiyar.
A yanzu haka dai ana sa ran tsohon kocin Bayern Munich da Jamus, Hansi Flick ne zai maye gurbin Xavi a matsayin kocin Barcelona.