Barcelona ta sayi Jules Koundé daga Sevilla

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cim ma yarjejeniya da takwararta ta Sevilla don dauko dan wasan bayanta, Jules Koundé, a kan kudi sama da Fam miliyan 50. A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana yadda dan wasan ya gama cim ma matsaya da kungiyar ta Barcelona. Majalisa ta yi sammacin Emefiele bayan […]

Barcelona ta sayi Jules Koundé daga Sevilla

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta cim ma yarjejeniya da takwararta ta Sevilla don dauko dan wasan bayanta, Jules Koundé, a kan kudi sama da Fam miliyan 50.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana yadda dan wasan ya gama cim ma matsaya da kungiyar ta Barcelona.

A baya dai kungiyar Chelsea ta kasar Ingila ta yi kokarin daukar dan wasan a kan kudi Fam miliyan 55 kamar yadda rohatanni suka nuna.

Sai dai dan wasan ya nuna bai da ra’ayin taka leda a kasar ta Ingila.

Wannan dai shi ne kusan karo na uku da Barcelona ke kasa kungiyar Chelsea a wajen sayen ’yan wasa, na baya-bayan nan dai shi ne dan wasan gaban Leeds United dan asalin kasar Brazil wato Raphinha da Barcelona din ta siya a lokacin da Chelsea ke dab da daukarsa.

Hakazalika shi ne dan wasa kusan na biyar da Xavi ya siyo a kakar wasar bana, a wani yunkuri na ganin ya dawo da martabar kungiyar ta Barcelona a idon duniya.