Barcelona ta tsallake rijiya da baya a wasan mako na shida a La Liga
Barcelona ta koma ta daya a kan teburin La Liga da maki 16.
Barcelona ta tsallake rijiya da baya a wasan mako na shida na La Liga da suka fafata da Celta Vigo a filin wasa na Estadi Olímpic Lluís Companys.
Barcelona wacce ta farke dukkan kwallayen da aka jefa a komarta har da kari, ta doke Celta Vigo 3-2 a wasan na ranar Asabar a Sifaniya.
- An kashe fararen hula 5 a birnin Timbuktu
- Matsalar rashin zuwan mata makaranta ta fi tsanani a Arewacin Najeriya — UNICEF
Jorgen Strand Larsen ne ya fara ci wa Celta Vigo kwallo a minti na 19 da fara tamaula, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Anastasios Douvikas ya kara na biyu.
Sauran minti tara a tashi daga wasan Barcelona ta fara farke kwallayen, inda Robert Lewandowski ya zura biyu a raga, sannan Joao Cancelo ya kara na uku daf da za a tashi daga fafatawar.
Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta daya a kan teburin da maki 16 kafin Real Madrid mai maki 15 ta buga wasanta.
Ranar Lahadi Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan hamayya a karawar mako na shida.
Ranar Talata Barcelona za ta je gidan Real Mallorca a karawar mako na bakwai a La Liga.
Ita kuwa Celta Vigo za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ranar Alhamis a dai wasan babbar gasar tamaula ta Sifaniya.