Barcelona ta yi canjaras da Rayo Vallecano
Unai Lopez ya fara zirara wa Barcelona kwallo a ragar ta a mintina 39 da fara wasan.
Kungiyar Barcelona ta yi canjaras 1-1 a karawar da ta yi da Rayo Vallecano, sakamakon da ya sake tabbatar mata da matsayi na 3 a teburin La Liga da maki 31.
Unai Lopez ya fara zirara wa Barcelona kwallo a ragar ta a mintina 39 da fara wasan, yayin da ta farke cin a mintina na 82, sakamakon kuskuren da Florian Lejeune ya yi wajen jefa kwallo a ragarsu.
Mai horar da ‘yan wasan Barcelona Xavi Hernandez, ya sauya ‘yan wasa guda 6 daga cikin kungiyar da ta doke Alavez kafin tafiya hutun mako guda, amma kuma hakan bai sa su samun nasara a kan Vallecano ba wadda ke matsayi na 9 a teburin La Liga.
Wannan farkewar ce ta hana Vallecano samun nasara a kan Barcelona wadda ke rike da kofin gasar La Liga na kakar da ta gabata.
A ranar Litinin mai zuwa ake saran Girona wadda ke matsayi na farko da maki 34 za ta kara da Athletico Bilbao, yayin da Real Madrid da ke matsayi na biyu da maki 34 zata kara da Cardiz gobe Lahadi.