Barcelona za ta dauke Juan Mata daga Chelsea

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen a shekaranjiya Laraba ne ya nanata kudurinsa na dauke dan wasan Chelsea Juan Mata kafin a fara kakar wasa mai zuwa.Kulob din ya ce tuni ya ware Fam miliyan 30 don ganin ya saye dan wasan wanda sabon kocin Chelsea Jose Mourinho ya bayyana cewa da wuya ya […]

Barcelona za ta dauke Juan Mata daga Chelsea
Barcelona za ta dauke Juan Mata daga Chelsea

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen a shekaranjiya Laraba ne ya nanata kudurinsa na dauke dan wasan Chelsea Juan Mata kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Kulob din ya ce tuni ya ware Fam miliyan 30 don ganin ya saye dan wasan wanda sabon kocin Chelsea Jose Mourinho ya bayyana cewa da wuya ya yi amfani da dan wasan a shirye-shiryensa na tunkakar kakar wasa mai zuwa.
Duk da irin namijin kokarin da Mata ya yi a kakar wasan da ta gabata, sabon kocin Chelsea Mourinho ya nuna Mata ba irin dan wasan da yake bukata a kulob din ba ne.  Hasalima ya ce ya gwammace ya yi amfani da Eden Hazard a kulob din ne fiye da Juan Mata don haka kulob din FC Barca suka yanke shawarar dauke dan wasan kafin a yi musu shigar sauri.
Kulob din Barcelona dai ya bayyana cewa tuni ya fara shirin yin garambawul ga ’yan wasansa don haka akwai yiwuwar kulob din ya sayar da wasu daga cikin ’yan wasansa irin su Cesc Fabgregas da Dabid billa da Thiago Alcantara da sauransu kafin a fara kakar wasa ta bana.