Barcelona za ta yi asarar kudin shiga saboda gyaran Camp Nou

Za a soma aikin a kakar wasa ta gaba zuwa watan Nuwamba na 2024.

Barcelona za ta yi asarar kudin shiga saboda gyaran Camp Nou

Magoya bayan Barcelona

Barcelona za ta yi asarar kusan €55m ($60.7m) na kudin-shigarta idan aka rufe babban filin wasanta na Camp Nou don yin gyare-gyare.

A makon jiya ne kafofin watsa labaran Sifaniya sun rawaito cewa kungiyar za ta koma karamin filin wasa na Lluis Companys Olympic da ke Montjuic yayin da ake gyara Camp Nou.

Mataimakiyar shugaban Barcelona Elena Fort ta bayyana yadda kwaskwarimar da za a yi wa filin wasan za ta kasance, tana mai cewa za a soma aikin a kakar wasa mai zuwa daga watan Yuni har karshen watan Nuwamba na 2024.

Fort ta ce za su yi amfani da kujeru 49,472 don gudanar da kasuwanci a filin wasa na Lluis Companys Olympic, wanda ke iya daukar ‘yan kallo 54,367.

Ta kara da cewa sun kulla yarjejeniya da masu zuba jari 20 da za su dauki nauyin gudanar da gyare-gyaren a kan kusan €1.45b.

Za a yi kwaskwarimar ce tsawon shekaru da suka kama daga 5, 7, 9, 20 da 24.