Barceona na maraba da Pep Guardiola
A hirar da jaridar La Republica ta Spain ta yi da Shugaban Kulob din FC Barcelona, Maria Joseph Bartomeu a ranar Talatar da ta wuce ya ce har yanzu kulob din yana maraba da Pep Guardiola tsohon kocin kulob din a duk lokacin da ya nemi ya koma. Ya ce kofa a bude take a duk […]
A hirar da jaridar La Republica ta Spain ta yi da Shugaban Kulob din FC Barcelona, Maria Joseph Bartomeu a ranar Talatar da ta wuce ya ce har yanzu kulob din yana maraba da Pep Guardiola tsohon kocin kulob din a duk lokacin da ya nemi ya koma. Ya ce kofa a bude take a duk lokacin da kocin ya nemi sake horar da kulob din.
Pep Guardiola wanda ya taso daga kulob din Barcelona na matasa har ya horar da babbar kungiyar, ya kasance daya daga koci-kocin da suka kafa tarihi wajen lashe kofuna a kulob din.
Bayan ya bar kulob din ya horar da kulob din Bayren Munich na Jamus kuma yanzu haka shi ne kocin kulob din Manchester City na Ingila.
Sai dai ganin yadda yake fuskantar kalubale a City ya sa ake rade-radin zai bar kulob din a karshen kakar bana.
Wannan ya sa FC Barcelona ta fara zawarcin kocin ganin akwai yiwuwar su yi ban-kwana da kocinsu na yanzu Ernesto Balberde a karshen kakar wasar bana.