Barci ko alwalla?
Wani malamin makaranta ne da ke koyar da Fikihu, ya je aji sai ya rubuta maudu’in da zai koya masu a kan allo, kamar haka: Abubuwan da ke karya alwala.’ Yana gama rubutawa sai ya koma kan kujera, ya kama barci. Can sai ga jami’an duba makaranta sun zo daga ma’aitakatar ilmi. Da suka shiga […]
Wani malamin makaranta ne da ke koyar da Fikihu, ya je aji sai ya rubuta maudu’in da zai koya masu a kan allo, kamar haka: Abubuwan da ke karya alwala.’ Yana gama rubutawa sai ya koma kan kujera, ya kama barci. Can sai ga jami’an duba makaranta sun zo daga ma’aitakatar ilmi. Da suka shiga ajinsa sai suka tarar da shi yana barci. Da suka yi masa magana sai ya nuna kamar bai gan su ba. Can sai ya yi firgigi ya tashi, sai y ace wa dalibai: “Yauwa, yara kun ga kamar irin wannan barcin, shi ma yana karya alwala.” (Wato ya nuna wa jami’an cewa ba barci yake ba, misali yake bayarwa).
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382