Barci ya kwashe barawo a cikin motar da ya yi sata
Jami’an tsaron a Atlanta ta kasar Amurka sun kama wani mutum mai suna Timothy Zacharie dan shekara 23 da ake zargin ya saci katin cire kudi da katin shaida a motoci takwas, bayan da barci ya kwashe shi a daya daga cikin motocin da ya yi wa satar. Ofishin babban jami’in ’yan sandan yankin Cherokee […]
Jami’an tsaron a Atlanta ta kasar Amurka sun kama wani mutum mai suna Timothy Zacharie dan shekara 23 da ake zargin ya saci katin cire kudi da katin shaida a motoci takwas, bayan da barci ya kwashe shi a daya daga cikin motocin da ya yi wa satar.
Ofishin babban jami’in ’yan sandan yankin Cherokee ya ce, jami’an tsaro sun kama Zacharie ne a ranar Talata bayan da mataimakinsa ya kama shi yana barci cikin wata mota da aka ajiye a kusa da makwabtansa.
Ofishin dai nada masaniya a kan wani ya yi sata a cikin motoci daga bisani aka gano Zacharie lokacin da ake bincike a yankin. Masu binciken sun gano kudaden sata da katin kyauta mallakar wadansu mazauna yankin a hannunsa. Ana dai tuhumar Zacharie a kan laifuffukan da suka hada: fasa taga sai dai babu wani lauya da ya tsaya masa don mayar da martini. Makwabatan da suke kusa da Zacharie sun kai nisan kilomita 48 a Arewa maso Yammacin jihar. .Atlanta a Amurka.