Barden Ibadan ya jinjina wa gwamnonin Katsina da Zamfara kan sulhu da ‘yan bindiga

Wani shugaban al’umma a Ibadan ya yi tir da masu kushe matakin sasantawa da ’yan bindiga da wadansu gwamnoni Arewa ke yi. Shugaban al’umma a Ibadan kuma daya daga cikin hakimai a Masarautar Hausawan Ibadan Alhaji Ibrahim Haruna (Barde) ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Zamfara da Katsina su ci gaba da daukar matakin sasantawa […]

Barden Ibadan ya jinjina wa gwamnonin Katsina da Zamfara kan sulhu da ‘yan bindiga

Wani shugaban al’umma a Ibadan ya yi tir da masu kushe matakin sasantawa da ’yan bindiga da wadansu gwamnoni Arewa ke yi.

Shugaban al’umma a Ibadan kuma daya daga cikin hakimai a Masarautar Hausawan Ibadan Alhaji Ibrahim Haruna (Barde) ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Zamfara da Katsina su ci gaba da daukar matakin sasantawa da ’yan bindiga domin kawo karshen matsalar kashe-kashen rayuka da satar mutane da fashi da makami a jihohinsu. Ya ce, “Sasantawar da gwamnonin jihohin suke yi domin samo mafita kan wannan matsala ce mafi alheri a kasa baki daya.”

Barden Ibadan, ya fadi haka ne a zantawarsa da Aminiya inda ya ce, “Masu sukar wannan mataki sun kasa kawo hanyar gyara a kan wannan lamari. Wato suna so a ci gaba da kasancewa cikin matsalar tsaro da kuncin rayuwa a Najeriya. Ya kamata dukkanmu mu roki Allah Ya kawo nana mafita kan wannan matsala kuma mu bayar da shawara mai amfani da za ta kai ga cimma nasara domin mu da kanmu ne za mu lalubo hanyar gyara Najeriya.”

Dangane da wasu sharudda da ’yan bindiga suka gindaya kafin su ajiye makamai, sai Barde Ibrahim Haruna ya ce, “Dukkan matakan sulhu ana tsara su daki-daki ne kuma gwamnonin jihohin da jami’an tsaro suna da hikima da basirar daukar matakin da ya dace. Misali masu cewa, sai an sako mutanensu da aka tsare kafin su ajiye makami, mahukunta za su duba su gani tare da yin bincike domin gano mutanen da suka cancanta a sallama. Wadanda ba su cancanta ba sai a hukunta su kamar yadda dokar kasa ta tanada daidai da irin laifin da suka aikata.”

A kan sabuwar rundunar yaki da masu satar mutane (IRT) a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamsihinan ’Yan sanda Abba Kyari a karkashin ofishin Sufeto-Janar Barde Ibrahim Haruna ya ce, “Ya wajaba a jinjina wa rundunar kan bullo da sababbin dabarun gano maboyar masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka da kama su, wanda hakan ya sa aka samu saukin aukuwar wannan barna idan aka kwatanta da na baya.” Ya kawo shawarar bude ofisoshin rundunar IRT a dukkan jihohin kasar nan domin dakile miyagun ayyuka a cikin kasa.

Kuma ya yi kira ga dukkan ’yan Najeriya su bayar da hadin kai da goyon baya ga sabon shirin tsaro wanda ya ce, “A matsayina na dan adawa tsakani da Allah ina ganin Gwamnatin Tarayya ta taka rawar gani a kan tsaron kasa.”