Bare United za ta ci gaba da fafatawa duk da rashin shiga Rukuni na Daya na  ’Yan dagaji

Kungiyar kwallon kafa ta Bare United da ke garin Billiri a Jihar Gombe za ta ci gaba da fafatawa a wasa don ganin ta cimma burinta duk da ba ta samu hayewa Rukunin na 1 na ajin ’yan dagaji na kasa. Sakataren Kungiyar Umar Billiri ya karin ce wannan rashin nasara da  ba su samu […]

Bare United za ta ci gaba da fafatawa duk da rashin shiga Rukuni na Daya na  ’Yan dagaji
Bare United za ta ci gaba da fafatawa duk da rashin shiga Rukuni na Daya na  ’Yan dagaji

Kungiyar kwallon kafa ta Bare United da ke garin Billiri a Jihar Gombe za ta ci gaba da fafatawa a wasa don ganin ta cimma burinta duk da ba ta samu hayewa Rukunin na 1 na ajin ’yan dagaji na kasa.

Sakataren Kungiyar Umar Billiri ya karin ce wannan rashin nasara da  ba su samu hayewa ba a wannan karo ba abu ne da zai sanyaya musu gwiwa ba. “Mun yi bakin kokarinmu a yanzu amma za mu koma mu sake duba kura-kuranmu sannan mu shirya a nan gaba,” inji shi.

Umar ya yi kira ga masu hannu da shuni da kuma mahukuntan Karamar Hukumar Billiri su taimaka Wa kungiyar da tallafin kudi domin a halin yanzu kusan mutum daya ne yake daukar nauyinta.

“Muna kira ga mahukuntan Karamar Hukumar Billiri su tallafa wa wannan kungiya da kudi, domin a halin yanzu Shugaban Kungiyar Alhaji Alhassan Galadima ne kadai yake daukar dawainiyarta,” inji shi.