Barin kashi a ciki bai maganin yunwa

Akan ce amfanin hankali aiki da shi, domin kuwa shi ne ke bambanta mutum da dabba. Wanda duk ya rasa hankali, to zai gamu da batan basira, daga nan kuma sai ya shiga wadari a duhu, sa’annan ya shiga kame-kame da karairayi kamar wanda ya harbi kura. Irin halin da Babban Jami’i Mai Shawartar Shugaban […]

Barin kashi a ciki bai maganin yunwa
Barin kashi a ciki bai maganin yunwa

Akan ce amfanin hankali aiki da shi, domin kuwa shi ne ke bambanta mutum da dabba. Wanda duk ya rasa hankali, to zai gamu da batan basira, daga nan kuma sai ya shiga wadari a duhu, sa’annan ya shiga kame-kame da karairayi kamar wanda ya harbi kura.

Irin halin da Babban Jami’i Mai Shawartar Shugaban kasa Game da Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) ya fada ciki ke nan a ‘yan kwanakin nan domin kuwa ya gwammace ya daure wa karya gindi, ya kuma dukufa bisa al’amuran yaudara don ya taimaka wa kokarin da iyayen gidansa ke yi na cutar da talakawansu. Yayin da daukacin ‘yan Najeriya suka kosa zagayowan lokacin zabe su sake zagayowa, domin sun tabbatar za su samu sukunin yin canjin da zai inganta matsayinsu, ya kuma amfani rayuwarsu, sai ga Kanar Sambo ya tsallake zuwa kasar Birtaniya, inda ya kira taron manema labarai a Catham House, wurin da ya shahara wajen daukan matakan da Turawan mulkin mallaka suka dade suna yi don tadiye kasashe masu tasowaya.
A cewar Kanar Sambo, rashin ingantaccen tsaron da ke wanzuwa a wasu sassan kasar nan na iya kawo cikas ga gudanar da zaben a wannan sashin, sa’annan kuma kaman yadda ya hakikance, hukumar zabe ba ta shirya yadda ya kamata ba, domin kuwa akwai mutane kusan miliyan talatin da ba su samu katunansu na jefa kuri’a ba har yanzu. Ya kara da cewa wai gudanar da zabubbukan a daidai lokacin da aka tsara zai iya janyo gagarumar matsalar da za ta haddasa yamutsi da rashin kwanciyar hankali, saboda haka nan sai ya bayar da shawarar a gurgusa da zabubbuka zuwa kwanakin talatin kafin rantsar da zababbun shugananni.
Wannan batu na Kanar Sambo ya ba kowa mamaki, ganin cewa idan ba da yawun gwamnatin Goodluck Jonathan ne ba ba yadda za a yi ya yi irin wannan furuci, domin hakan shiga sharo ba shanu ne. Baicin haka nan da wane dalili ne Kanar Sambo zai bayar da shawara mai rikitarwa kaman haka a can kasar Birtaniyya, maimakon a Abuja ko Lagos, idan dai ba wani sako ne na musamman yake son mika wa Turawa ba? Bar ta wannan! Aikin Kanar Sambo shi ne bayar da shawara game da harkokin da suka shafi tsaro ba na yadda ake gudanar da zabe ba. An ce wanda ke sanye da takalmi shi ya san inda ya matse shi, to Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Attahiru Jega bai fito fili ya fayyace wadancan matsalolin da Kanar Sambo ya rattaba ba, to don me zai ari bakinsa, ya ci masa albasa da shi?
Dangane da haka nan Hukumar zabe ta fito firi-falo ta fayyace cewa ba abin da zai hana wadannan zabubbukan gudana yadda aka shirya, domin kuwa tana nan tana kokarin samar da katunan zaben ga sauran jama’ar da ba su amshi nasu ba ta hanyar sassauta matakan aikewa da su kurkusa da masu bukatarsu. A game da batun rashin tsaron da Kanar Sambo ke cewa zai iya dagula tsarin gudanar da zaben kuwa ana iya cewa bai san da haka ba ne sai a yanzu da jam’iyyar da ke da gwamnati, wacce yake yi wa aiki ta fahimci cewa ruwa ya kare wa dan kada sa’annan zai kawo wannan a matsayin hujjarsa na dage lokacin zaben zuwa gaba? Batun rashin tsaro dai ba wata matsala ba ce, domin idan gwamnatin har da gwamnatin Jonathan na son a kwantar da kurar da ‘yan ta’adda ke tayarwa a shiyyar Arewa-maso-Gabas, ai da tuni haka ya zame tarihi. Da gangan aka kyale ta’addancin ya tabarbare don a kafa hujjar dage zabe ko gurgusawa da lokacinsa gaba
Ai ko ba komai mun ga yadda aka gudanar da zabubbuka a kasashen da ake gumurzu da yake-yaken da suka fi na Najeriya kazancewa, kuma ko kadangare ba a kashe ba yayin da ke jefa kuri’ar. To sai a Najeriya ne za a nemi a yi haka, don dai kawai a ba jam’iyyar PDP da shugabanin gwamnatinta damar tsara sabuwar kutungwilar da za ta agaza mata wajen tafka magudin zaben da zai kai ta ga nasara ko tayar da fitinar da za ta hana zabubbukan gudana?
Da wane lalili ne Kanar Sambo zai ce hukumar zabe ba ta shirya yadda ya kamata ba, tun da ba shi ne ke da hakkin sanya ido bisa kan aikace-aikacenta ba? Bai ji kunyar kaje wannan batu ba, ganin cewa idan har ya nuna kasawar hukumar zabe, to ya tabbatar da kasawar gwamnatin tarayya ke nan? To me zai sa ya yi kirari, sa’annan ya kirba wa cikinsa zabgegiyar wuka? Hakan ya kara tabbatar da cewa Gwamnatin Jonathan ba ta san abin da take yi ba, domin ba ma ga samar da katuttukan jefa kuri’a ne ba kadai ta kasa yin wani katabus, haka nan ne ma take yi a dukkan sauran katuttukan da ta alkawarta za ta samar ga ‘yan kasa don tabbatar da halaccinsu a kasar haihuwarsu da sauran ire-irensu.
To ‘yan Najeriya sun fahimci haka, sun kuma tashi haikan don nuna kin amincewarsu da batun gurgusawa da ranakun zaben gaba, gudun kada a kwata abin da aka yi a zaben 2011, sa’ilin da aka dage zaben a ranar farko da mako guda, kuma hakan ya ba gwamnatin tarayya damar tayar da hankali don a gudanar da zaben a wasu jihohi yadda take so.
A yanzu ma sauran kasashen duniya sun san cewa shawarar da Kanar Sambo ya kawo game da gurgusawa da ranakun zaben ihu ne bayan hari, kuma hatta Amurkan da ake ganinta a matsayin uwargijiyar Gwamnatin Jonathan ta ce wajibi ne a gudanar da zabubbukan kan kari, kuma ta yi kashedi game da tayar da kayar baya game da sakamakon da zai biyo baya. Bisa ga dukka alamu guguwar canji ce ke bugawa, wanda kuma duka ya rutsa da ita zai tsira, wanda ya ki, ya tsaya kikam, za ta karya shi baras.To idan kuwa haka ne ashe kanar Sambo kunshi ne kawai ya yi a baraka, zabe sai an yi shi, domin barin kashi a ciki bai maganin yunwa, abin da ake gudu kuma sai ya afku da ikon Allah.