Barista Dogara ne injin tafiyar APC a Jihar Bauchi – Iliyasu Zwall

Kwamared Iliyasu Ibrahim Zwall tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi daga mazabar Lere/Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa, a yanzu shi ne Babban Mai tallafa wa Shugaban Majalisar Tarayya Honarabul Yakubu Dogara, a tattaunawarsu da wakilinmu ya bayyana abubuwan da Yakubu Dogara ya yi ga mazabarsa: Me za ka ce game da tafiye-tafiyen da Shugaban […]

Barista Dogara ne injin tafiyar APC a Jihar Bauchi – Iliyasu Zwall
Barista Dogara ne injin tafiyar APC a Jihar Bauchi – Iliyasu Zwall

Kwamared Iliyasu Ibrahim Zwall tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi daga mazabar Lere/Bula a karamar Hukumar Tafawa balewa, a yanzu shi ne Babban Mai tallafa wa Shugaban Majalisar Tarayya Honarabul Yakubu Dogara, a tattaunawarsu da wakilinmu ya bayyana abubuwan da Yakubu Dogara ya yi ga mazabarsa:

Me za ka ce game da tafiye-tafiyen da Shugaban kasa Buhari ke yi?
A fahimtata kasashen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zuwa tun lokacin da aka zabe shi yana zuwa ne domin ganin ya kawo wa Najeriya ci gaba musamman kwato kudaden da aka sace aka kai kasashen waje aka ajiye. Don haka sai ya nemi goyon bayan kasashen kafin gwamnati ta amso kudaden ta zo ta gudanar da ayyuka na musamman da su.
Wasu abubuwa ne Dogara ya yi ga mutanen mazabarsa?
Babu lokacin da zan iya lissafo maka dukkan ayyukan alheri da Dogara ya yi ga mutanen mazabarsa sai dai in fada maka kadan daga cikin ayyukan kowa ya sani a Najeriya tun yana dan majalisa yake tura yara zuwa kasashen waje domin karo ilimi ya kuma tona bohul-bohul masu dimbin yawa. Akwai matasa Musulmi da Kirista ya taimake su a rayuwa, bayan ya gina masallatai masu dimbin yawa. A lokutan bukukuwan Babbar Sallah masallatai da dama yana ba su gudunmawar shinkafa da ragunar layya. Allah ne kawai Ya san adadin masallatan da Honarabul Dogara ya gina a Jihar Bauchi. Wajen tallafa wa al’umma ba ya nuna wani bambanci, kai Musulmi ne ko Kirista ya dauki kowa nasa ne a siyasance. Yanzu haka akwai yara da dama da suka kawo min takardunsu suna neman tallafin karatu kuma ina tabbatar maka cewa zai taimaka bakin gwargwado. Akwai asibitoci da dama da muka ba su gudunmawar kayayyakin aiki da magunguna.
Da gaske ne akwai wasu daga cikin ’ya’yan Jam’iyyar APC a Bauchi da ba sa jituwa da Dogara?
Babu wani dan Jam’iyyar APC da zai nuna yatsa ga Honarabul Yakubu Dogara domin yana daya daga cikin wadanda suka yi amfani da hikima da ilimi da lokaci da kudinsu wajen kafa Jam’iyyar APC. Tun kafin a yi mata suna bayan haka, ya ba da gudunmawa sosai wajen kawar da gwamnatin baya. Tun daga matakin jiha har zuwa tarayya. Honarabul Dogara yana da mutunci a wajen al’umma kuma babu wanda ya kai shi wahala ga Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, kusan za mu iya cewa ya riga kowa shiga APC. Amma duk da haka akwai wadanda ya taimake su amma daga bisani suka koma suna yakarsa a siyasance.
Honarabul Dogara ne injin tafiyar APC a Jihar Bauchi kuma duk wani dan APC ya san wane ne Yakubu Dogara, babu wanda zai yi masa gori domin ya ba da gudunmawa daidai gwargado har zuwa lokacin da APC ta kafa gwamnati a zaben 2015.
Mene za ka ce ga ’yan siyasa masu sukar gwamnatin APC?
Ina mamakin yadda wasu marasa kishin kasa suke sukar manufofin Shugaban kasa, shekara 16 aka yi ana lalata dukiyar al’umma saboda haka cikin wata 10 sai mutane sun yi hakuri kafin abubuwa su inganta. barnar da aka yi a kasar nan tana da yawa saboda haka muna ba da hakuri ga mutane gwamnatocin baya sun saba ba da kudi haka kawai yanzu kuma ana gyara ne.
Ya kamata mutane su fahimci cewa sukar shugabanni ba ya da wani amfani, domin idan shugaba ya lalace wadanda za su fara shan wahala su ne talakawa da marasa karfi. Ina kira ga matasa don Allah a nemi sana’a kuma a hada da hakuri domin gwamnatin APC ta sha bamban da gwamnatocin baya. Akwai matasa da dama da suka kashe zuciyarsu ba su da wani aiki sai yawon roko a tsakanin jama’a, an wuce lokacin da mutum zai wanke rigarsa ya fita neman kudi a wajen ’yan siyasa. A koya maka yadda ake kama kifi ya fi a ba ka kifin a gashe, wannan shi ne abin da zan fada a takaice.
 Na je kasashe da amma ban taba ganin kasar da ta kai Najeriya arzikin kasa ba, kuma ya kamata matasa su fahimci cewa akwai riba sosai a noma kuma duk kasar da matasa suke noma talauci yana raguwa a tsakanin jama’a.  Yau kasar Ghana tana daya daga cikin kasashen Afirka da suke bunkasa a fannin tattalin arziki.
A karshe mene ne sakonka ga jama’a?
Babban sakona shi ne ya kamata mu ci gaba da addu’a ga shugabanni, bayan haka mutane su cire kwadayi a kan masu mulki. Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban Majalisar Tarayya, Honarabul Dogara suna da manufofi masu kyau na ingata rayuwar al’umma. Muna godiya ga Allah bisa yadda aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar Arewa maso Gabas wadanda suka rasu sakamakon tashe-tashen hankular yankin Allah ya gafarta musu. Allah Ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Bauchi da Najeriya baki daya.