Barka da cire shingayen sojoji a kan tituna
A makon jiya ne Shugaban kasa Buhari Muhammadu ya bai wa Babban Hafsan Tsaro, Iya Mashal Aled Badeh umurnin a cire duk wani shigen bincike da ke kan titunan fadin kasar nan. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata ganawa da manyan hafsoshin, inda ya ce hakan ya zama wajibi saboda matsalolin da masu tafiye-tafiye […]
A makon jiya ne Shugaban kasa Buhari Muhammadu ya bai wa Babban Hafsan Tsaro, Iya Mashal Aled Badeh umurnin a cire duk wani shigen bincike da ke kan titunan fadin kasar nan. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wata ganawa da manyan hafsoshin, inda ya ce hakan ya zama wajibi saboda matsalolin da masu tafiye-tafiye suke fuskanta a shingayen. Babban Sakatare a Ma’aikatar Tsaro ta kasa, Mista Aliyu Ismaila, lokacin da yake ganawa da manema labarai, ya ce an dauki matakin ne saboda a bai wa ’yan sanda damar tafiyar da harkokin tsaron cikin gida. Har ila yau, matakin bai shafi Jihohin Barno da Yobe da kuma Adamawa ba bisa la’akari da yanayin tsaron da jihohin ke ciki.
Har ila yau, an cimma matsayar cewa sojojin za su ci gaba da tsayawa a muhimman shingayen bincike domin bincikar ababen hawa lokacin da bukatar hakan ta taso. Bugu da kari, za a samar da na’urar binciken ababan hawa. Kodayake, kwana guda bayan ba da wannan umurnin, babu wani sauran shingen binciken da ya rage a titunan fadin kasar nan. Sufeto Janar din ’yan sanda Solomon Arase ya ce za a samar da motocin sintiri guda 158 a duk fadin kasar nan domin magani duk wata barazanar tsaro da ka iya bijirowa. Ya ce, “mun shirya tsaf; za mu samar da motocin sintiri 158 domin maye gurbin da sojojin suka bari. Mun rigaya mun samar da guda 350. Idan aka hada da wadanda za mu kara guda 158, muna ganin za su inganta tsaro matuka.” Daga nan ya ce cire shingayen binciken ba yana nufin cewa daga yanzu ’yan sanda ba za su kara aiki tare da sojoji ba. Ya ce: “Kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukata, yakamata ya yi su tallafa mana a duk lokacin da muka nemi hakan. Aikinmu da su ya yi kama da aikin gayya.”
Galibin jama’ar kasar nan sun yi maraba da matakin cire shingayen musamman ganin yadda hakan zai saukaka zirga-zirga. Yawancin mutane suna ganin cewa ba ya ga mawuyacin halin da shigayen ke jefa su, babu wani tasiri da suke wajen dakile kowace barazanar tsaro. Kamar yadda suke bayyanawa, jami’an ba sa aikinsu irin yadda ya kamata saboda ba a taba kama wani, ko wani makami ba a shigayen. Sai dai ma a lokuta da dama, mayakan kungiyar Boko Haram sun sha kai hari a shigayen, inda suke kashe sojojin da ke aiki da kuma karbe musu makamansu.
A baya wani tsohon soja ya taba sukar kasancewar sojojin a shingayen binciken, inda ya ce suna aikin da ba su da horo akai. Baya ga wannan, akwai zargin cewa sojojin na karbar na goro, wanda hakan ya fara zubar masu da mutuncinsu a idon jama’a. Saboda irin wadannan dalilai, cire shingayen binciken abin a yi maraba da shi ne, musamman ma idan za a mayar da sojojin da suke wannan aikin zuwa yankin Arewa-maso-Gabas domin su tallafa wajen fafatawa da ’yan Boko Haram.
Har ila yau, yana da kyau a fahimci cewa kasar nan ta samu nasara da sosai a yaki da kungiyar, amma ba lokaci ne da za a kwanta a saki jiki ba. Yamata mahukunta su tabbatar da cewa cire shingayen bai haddasa wata kafa da matsalar tsaron za ta kara kunno kai. Jami’an tsaro su kara daura damara domin tabbatar da hakan bai, bai wa mayakan Boko Haram wata dama ba. Har ila yau, muna kira ga al’ummar kasar nan da su bai wa jami’an tsaro goyon baya, saboda bayan cire shingayen, za a dauki wasu sabbin matakai da ke bukatar goyon bayan kowa da kowa domin a cimma nasara. Ya dace ’yan Najeriya su fahimci cewa yakamata su kara hakuri da hukumomi, musamman ma akan matakan tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.
Har ila yau, ’yan sanda yakamata su fahimci cewa a yanzu alhakin kare al’umma ya koma kansu. Don haka ya dace su tashi tsaye. Kuma dalilin da ya sa a baya aka shigar da sojoji cikin harkar tsaron cikin gida shi ne saboda karancin jami’ai daga bangaren rundunar ’yan sandan kasar nan. Wannan ba lokaci ba ne na ba da uzuri, wannan wata dama ce da rundunar ta samu na gyara kimarta a idon m jama’a. Sufeto Janar Solomon ya ce an sayo wasu motocin sintiri kuma za a kara sayo wasu, wannan abu mai kyau. Amma, har ila yau, yakamata a kara daukar jami’an tsaro da kayayyakin aiki da sauransu. Wajibi ne ’yan sandan su fahimci cewa ba za a kara amincewa da uzurin da suka sha ba da wa a baya, inda suke cewa babu mai a motarsu ko mota ta lalace. Yakamata ’yan sanda su yi wa kansu karatun ta-natsu, su kara himma wajen sauke babban nauyin da aka rataya musu.