Barka da  Kirsimeti

A ranar Talatar wannan mako  25 ga Disamba 2018 ne ranar Kirsimeti bana inda mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya suke bikin zagayowar ranar haihuwar Isah Almasihu (AS). Mabiya addinin Kirista a sassan duniya suna gudanar da shagulgula kamar yadda al’adunsu suke nunawa. Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Talata da Laraba wato 25 da […]

Barka da  Kirsimeti

A ranar Talatar wannan mako  25 ga Disamba 2018 ne ranar Kirsimeti bana inda mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya suke bikin zagayowar ranar haihuwar Isah Almasihu (AS). Mabiya addinin Kirista a sassan duniya suna gudanar da shagulgula kamar yadda al’adunsu suke nunawa. Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Talata da Laraba wato 25 da 26 ga Disamban nan a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukuwan Kirsimeti da ranar rarraba kyaututtuka.

Ranar tana da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya inda miliyoyin mabiya addinin Kirista da ma wadanda ba Kirista ba suke murnar zagayowar ranar. A kasasahe da dama ranar tana zama ta musamman wajen gudanar da wasu harkokin na musamman don nuna farin cikin zagayowar ranar, kuma ta kasance ranar da ake gudanar da addu’o’i da tsarkake zukata yayin da ake nuna wa ’yan uwa da abokan arziki kauna da tare da raba kyaututtuka ga abokai da ’yan uwa.

Babban darasin da ranar take koyarwa shi ne, muhimmancin sakon kauna wannan ne dalilin da ya sa a ranar ake tunawa da kaunar haihuwar Isah Almasihu (AS)  ta haifar. A lokacin da yake raye a duniya yana nuna kauna ga al’umma har da masu yin zunubi. Sai da a yanzu gwamnatoci ba su daukar darasin da za a iya koyo daga wurinsa, musamman a yanzu da mutum yake raye kafin mutuwarsa.

A wannan lokacin ne shugabannin duniya suke amfani da wannan damar wajen yin kira ga mutane kan su kaunaci junansu tare da hada kai domin samun zaman lafiya a duk fadin duniya. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya ’yan Najeriya murnar bikin Kirsimeti tare da yin kira a kan su kaunaci junansu kuma a samu hadin kai a tsakanin kabilun kasar don inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Gwamnonin jihohin Najeriya ma sun mika sakon taya murnar Kirsimeti ga ’yan Najeriya.

Sun bukaci ’yan Najeriya su zauna lafiya saboda muhimmancinsa ga kasar, musamman idan aka yi la’akari da halin da kasar take ciki a yanzu.

Najeriya tana fuskantar kalubale da dama a yanzu daga yankuna daban-daban da suka shafi mutanen kasar. Wadannan sun hada da kuncin rayuwa da na tattalin arziki da barazanar tsaron rayuka da dukiyoyi, damasu kai hare-hare a wasu yankunan kasar nan, musamman yankin Arewa maso Gabas da masu fasa bututun man fetur a yankin Neja Delta, gwamnati ta damu matuka da yanayin da ’yan Najeriya suke ciki.

Abin lura a nan shi ne yadda zaben badi ke karatowa wanda za a yi watan Fabrairu da Maris. Don haka a yanzu duk hankalin ’yan Najeriya ya karkata ne a kan zaben na gaba. Bikin Kirismeti na bana ya zo daidai da lokacin da ’yan Najeriya za su samu saukin rayuwa wajen gudanar da addu’o’i. Saboda yanayin da ake ciki shi ne zai ba da damar sanin abin zai faru nan gaba.

Kuma abin sha’awa shi ne jawabin da Shugaban Kasa ya yi lokacin gabatar da kasafin kudin badi a ranar Larabar makon jiya a zauren Majalisar Dokoki ta  Kasa, inda Shugaban Kasar ya ce, gwamnati ta ware wani kaso a cikin kasafin kudin badi don daukar matakai wajen magance kuncin rayuwa da wadansu  ’yan Najeriya suke ciki. A yayin  da ’yan Najeriya suke murnar bikin Kirsimetin  bana lokaci ne da za su kara son Allah fiye da sauran mutane. Barka da Kirsimeti ’yan Najeriya.