Barka da Sallah Gizagawan Najeriya (2)

Bagizage Ibrahim Hamisu daga Kano ne ya bude shirin da cewa:  “Gizagawa, barkanmu da Sallah, muna fata Allah Ya karbi ibadunmu.Wannan shiri an kirkire shi ne don Gizagawa su mika gaisuwar Barka da Sallah ga ’yan uwa Gizagawa da abokan arziki. Bari in fara zundumo gaisuwa da jinjinar ban girma ga jiga-jigan tafiya, wato Sharif […]

Barka da Sallah Gizagawan Najeriya (2)

Wadansu daga cikin jagororin Kungiyar Gizago, Daga dama, Bashir Yahuza Malumfashi, Aliyu Xanlabaran Zariya, Musa Namusamman, Alkwatanayi sai M.K. Adam Gombe

Bagizage Ibrahim Hamisu daga Kano ne ya bude shirin da cewa:  “Gizagawa, barkanmu da Sallah, muna fata Allah Ya karbi ibadunmu.Wannan shiri an kirkire shi ne don Gizagawa su mika gaisuwar Barka da Sallah ga ’yan uwa Gizagawa da abokan arziki. Bari in fara zundumo gaisuwa da jinjinar ban girma ga jiga-jigan tafiya, wato Sharif Auwal Falala da ke zaune a Babban Birnin Tarayya Abuja. Fatanmu dai ka rika zundumo mana falala mu ma. Sai Bashir Yahuza Malumfashi, madugu uban tafiya, ka sani ka huta. Sai dattijon arziki, Yunus Abdullah. Ban manta ka ba, babban abokina, ka san jirgi, jirgi ya sanka; wato Muntaka A. Hadi. Sai kuma agogo sarkin aiki, M. K. Adam. Sai Liman ka san Allah, Malam Auwal L. K. Sai wakilin dukiya, Yahaya Usman Maikatifa, sai Hajiya A’isha Lawan Tarauni. Sai Hajiya Lami Jos, sai kuma Habu Tsoho, dogo mai doguwar aniya tare da abokinka Auwal Tahir Sabongida, tica uban karatu.

Ban manta da kai ba mai kwarjini da hangen nesa, wato Nura Adamu Kano. Sai Abdul’aziz Baka Maula tare da abokinka Abu Maryam Bazazzagi.

Mutanen da yawa, bari in dan dakata a nan in bar ku ku mika naku gaishe-gaishen. Bismillah.”

Daga nan sai Abdullahi Alkwatonawi ya amsa, shi ma ya shimfida nasa gaishe-gaishen kamar haka: “Gaisuwar Barka da Sallah ga Shugaban Gizagawan Birnin Tarayya Abuja, Musa Aliyu Namusamman, ina gaida Malam Nasir G. Ahmad ’Yan Awaki Kano da Sunusi Hashim Katsina da Habu Tsoho Layin ’Yan Goro Malumfashi. Ban manta da kai ba, tsohon Sakataran Gizagawa na Kasa, Aliyu Danlabaran Zariya da Malam Zakariyya Se’eed, Shugaban Gizagawan Jihar Kaduna. Haka kai ma dan uwa abokin aiki, Yusuf Zamfara, ina kuma gaishe da Kabir Sakaina Malumfashi tare da daukacin Gizagawa maza da mata; da fatar duk kun yi Sallah lafiya. Allah Ya maimaita mana. Barka da Sallah ga babban Bagizagen Najeriya, Auwal Ahmad L. K. Ibadan da mai kaunar Gizagawan Najeriya, Muhammad Jungudo Adamawa da Malam Sulaiman Idris Soba Ondo. Ina gaida mai Bagizage Abubakar Hamisu Yankatsari tare da ASP Ado Iro Charanchi. Da fatar kun yi bikin Sallah cikin farin ciki da annushuwa!

“Ina mika gaisuwa ga Bagizage a Jihar Katsina, Malam Hamza Usman. In na dace kana kusa, ga gaisuwar Barka da Sallah gare ka, Shugaban Gizagawan Jihar Nasarawa, Suwailu Muhammad Gwari da Shugaban Gizagawan Jihar Oyo Yusuf Salisu, da Shugaban Gizagawan Jihar Ribas, Sa’idu Abubakar Badarawa. Haka kai ma na Gizagawan Jihar Sakkwato, Kasimu Shehu Lema, ka samu shiga. Tare da Shugaban Gizagawan Jihar Ogun, Uba Ahmad Soba. Haka kuma ina yi wa daukacin Gizagawan Zumunci na kowane sako, Barka da Sallah! Allah Ya amshi dukkan ibadojin da muka gabatar, Ya sanya mun dace da dacewarSa, amin!”

Shi ma Usman Gambo ya bayyana nasa sakon da cewa: “Gaisuwar Sallah ga daukacin Gizagawan kasa baki daya, Allah Ya maimata mana, Ya kuma amshi ibadunmu amin. Gaisuwa ga iyalina, Hajiya Zainab da Hajiya Bilkisu da sauran ’ya’yanmu.”

Yunus Abu Sultan daga Jihar Kano, shi ma ya zo da nasa kamar haka: “Muna gaishe da Sherrif Auwal Falala, sai Malam Yunusa Abdullah da Abdullahi Alkotanawi da Muntaka Abdulhadi Dabo da Namusammam da Danlabaran da M. K. Adam da Yusuf Zamfara da Malam Nasir G. Ahmad da Kabiru Ghali Abban Saudat da Kabir Sakaina da Ahmad Amoeba da Bakamaula da Naziru Tamburawa da Nuran Masoya da Wakilin Dukiya da Dattijo Audu Goro da Skeeper Kura da Abdullahi Yellow da Mas’ud Gwammaja da sauransu. Muna addu’ar Allah Ya maimaita mana.”

Yunus Abdullah shi ma ya shigo da cewa: “Ina taya daukacin Gizagawan Najeriya, manyanmu da kanana tun daga Madugu uban tafiya da iyayen kungiya, har zuwa ga tsofaffin shugabanni tare da masu jagorancinmu a yau; Allah Ya karbi ibadarmu, da fatar muna daga cikin wadanda aka gafarta mawa a wannan wata. Amin summa amin.”

Sai kuma Musa Namusamman  cewa ya yi: “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, kuma tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta (SAW). Bayan haka, ya ku ’yan uwa Gizagawan Zumunci; a madadin ni kaina da iyalina da daukacin Gizagawan Babban Birnin Tarayya Abuja, muna yi wa daukacin Gizagawan kasar nan fatan alheri ku da iyalanku da yi mana addu’ar Allah Ya karbi ibadunmu da muka yi a cikin watan da ya shude, wato Ramadan mai alfarma da albarka. Allahumma amin. ’Yan uwa Gizagawa, kama daga iyayen kungiya har zuwa kasa ina yi mana Barka da Sallah, Allah Ya maimaita mana!”