Barka da Sallah Manyan Gobe

Muna fata ba ku rika yi wa mahaifanku kuka kan batun kayan Sallah ba. Ya kamata ku duba halin da ake ciki, ku fahimta mahaifanku suna sonku, haka kawai ba za su ki yi muku dinkin sallah ba. A wannan makon na yi muku guzurin labarin Masunci da ‘ya’yansa. Muna fata za ku bi labarin […]

Barka da Sallah Manyan Gobe
Barka da Sallah Manyan Gobe

Muna fata ba ku rika yi wa mahaifanku kuka kan batun kayan Sallah ba. Ya kamata ku duba halin da ake ciki, ku fahimta mahaifanku suna sonku, haka kawai ba za su ki yi muku dinkin sallah ba. A wannan makon na yi muku guzurin labarin Masunci da ‘ya’yansa. Muna fata za ku bi labarin bi-da-bi don kwasar lagwadar darussan labarin. A sha karatu lafiya.
Naku Bashir Musa Liman

Labarin Masunci da ‘ya’yansa

Akwai wani masunci da yake matukar son ‘ya’yansa ‘yan biyu, Hassan da Hussaina, tun suna kanana mahaifiyarsu ta rasu. Hakan ya sanya ya auro wata matar, sannan ya roki alfarmar ta rika lura da su. Ta amince, amma abin da bai sani ba matar tasa ta tsani ‘ya’yansa.
Kullum da safe yakan shirya ya tafi kogi kamun kifi, inda ya fita ne sai matarsa ta rika musguna wa ‘ya’yansa, sannan ta rika yi musu barazanar kashe su idan suka fada wa mahaifinsu halin da ake ciki.
Hakan ya sa suka yi shiru, amma bayan wani lokaci sai mahaifinsu ya fahimci halin da suke ciki. Ya kira matarsa ya yi mata nasiha, amma al’amarin ya rika yin gaba.
Wata rana bayan ya tafi kogi sai matarsa ta dauki Hassan da Hussaina, sannan ta kai su daji ta jefar, suka rasa hanyar dawowa, haka suka ci gaba da tafiya ga yunwa, ga kishir ruwa, ga kuma tsoro saboda dare ya fara yi, suna cikin tafiya ke nan sai suka iso wata babbar bukkar mai cike da abinci da kuma kayan alatu, suka yi murna, sannan suka ci abinci.
Bayan wani lokaci sai suka ga wata tsohuwa ta dawo, ashe mayya ce. Daga nan dora tukunyar ruwan tsafi a murhu, sannan ta ce za ta dafa su, ta cinye su. A lokacin da take iza wuta ne, sai Hassan ya tura ta cikin tukunyar, ta fada cikin tukunyar ruwan zafi ya dafa ta, haka ta mutu.
Daga nan suka gaji kayan alatu. Bayan sun dawo gida ne mahaifinsu ya ga dukiyar da suka samu, sai ya rika farin ciki.
A karshe ya kori matarsa, bayan ya samu labarin abin da ta yi wa ‘ya’yansa.