Barka da warhaka Manyan Gobe 01
Ina fata kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin Sarki da manomi. Labarin na jan hankalin Manyan Gobe da su rika tunani kafin su amsa kowace tambaya. A sha karatu lafiya.Taku; Amina Abdullahi Labarin Sarki da manomi A wani lokaci da ya wuce akwai wani sarki da yake son aurar da ‘yarsa, hakan ya […]
Ina fata kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin Sarki da manomi. Labarin na jan hankalin Manyan Gobe da su rika tunani kafin su amsa kowace tambaya.
A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi
Labarin Sarki da manomi
A wani lokaci da ya wuce akwai wani sarki da yake son aurar da ‘yarsa, hakan ya sanya ya rika fafutikar nema mata mijin da ya dace da ita, dalilin da ya sa ya ba da sharadin duk wanda yake so ya auri ‘yarsa, sai ya amsa tambayarsa daidai.
Tambayarsa ita ce: mene ne yake sanya mutane kuka? Kowane saurayi ya yi iya kokarin amsa wannan tambayar amma ya kasa.
Rannan sai wani manomi ya iso fada, ya kuma bukaci a yi masa izini ya amsa tambayar sarki. Bayan an yi masa izini ne sai ya ce: “amsar ita ce,ruwa.” Sai aka ce masa ya yi bayanin abin da yake nufi da hakan. Sai ya ce, ruwa na sanya manomi farin ciki domin yana taimaka wa shukarsa. Amma ruwa na sanya maginin tukwane kuka saboda yana bukatar rana domin ya sayar da tukwanensa.
Sai abin ya ba sarki mamaki. Nan take ya ba shi ‘yarsa ya aura.
Da fatan Manyan Gobe za su kasance masu tunani kafin su amsa kowace tambaya aka yi musu musamman ma a makaranta.