Barka da warhaka Manyan Gobe 02

Ina fata kuna lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin bera mai son banza. Labarin na kunshe da yadda son banzar bera ta janyo masa ajalinsa.A sha karatu lafiya.Taku; Amina Abdullahi Labarin bera mai son banza Akwai wani bera mai son kansa sosai. Rannan sai ya ga kwandon masara, nan take kwadayinsa ya motsa, […]

Barka da warhaka Manyan Gobe 02

Ina fata kuna lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin bera mai son banza. Labarin na kunshe da yadda son banzar bera ta janyo masa ajalinsa.
A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi

Labarin bera mai son banza

Akwai wani bera mai son kansa sosai. Rannan sai ya ga kwandon masara, nan take kwadayinsa ya motsa, wanda ya sanya ya yi wata kofa a kwandon don ya samu hanyar da zai bi ya shiga don ya rika cin masara. Bayan ya yi kofar har ya samu shiga cikin kwando ne a maimakon ya ci daidai cikinsa, sai ya ci masara mai yawa har cikinsa ya girma ya kasa fita daga kwandon masarar.
Can sai ya fara kukan neman taimako. Ana cikin haka sai zomo ya karaso wurin, inda ya tambaye shi abin da yake damunsa, sai ya ce masa ya ci ya koshi ne ga shi kuma ya kasa fita daga cikin kwandon masarar. Sai zomo ya yi dariya, sannan ya ce to ya bari sai cikinsa ya sauka sannan ya fito.
A haka sai barci ya sace bera har gari ya waye. Da gari ya waye, a maimakon ya fita tun da cikinsa ya sabe, sai ya sake ci gaba da cin masara har sai da cikinsa ya sake girma. A nan ne bera ya tuna da cewa ba zai iya fita ba.
Jim kadan, sai kyanwa ta zo wucewa sai ta ji warin bera, tana bincikawa sai ta gan shi, ba tare da bata lokaci ba ta cinye shi.