Barka da warhaka Manyan Gobe…1
Yaya karatu? Ina fata kuna mayar da hankali ga karatu, domin jahili ba zai ci ribar zaman duniya ba. A wannan makon na kawo muku labarin ‘Mage da bera’. Ina fata za ku bi labarin sau-da-kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa.A sha karatu lafiyaNaku Kawu Bashir Musa Liman Labarin Mage da bera […]
Yaya karatu? Ina fata kuna mayar da hankali ga karatu, domin jahili ba zai ci ribar zaman duniya ba.
A wannan makon na kawo muku labarin ‘Mage da bera’. Ina fata za ku bi labarin sau-da-kafa don cin ribar darussan da yake koyarwa.
A sha karatu lafiya
Naku Kawu Bashir Musa Liman
Labarin Mage da bera
A wani lokaci da ya shude an yi wani sarki da ke mulki a kasar Gabas. Wannan sarki yana da barori da bayi masu yawa, yana da wata mage da ke tsaron taskarsa.
Ashe akwai wani bera da ke son wata ‘yar aikin gidan sarki. bera talaka ne, amma ita wannan ’yar aikin tana neman bera ya rika yi mata abubuwan da suka fi karfinsa. Hakan ne ya sa bera ya fara sata don ya biya mata bukatarta kasancewar yana matukar sonta.
Ana cikin haka ne sarki ya fahimci ana shiga taskarsa ana yi masa barna. Ya kira mage ya nemi bahasin abin da ke faruwa. Ta kuma yi masa alkawarin za ta gudanar da bincike, sannan ta cafke duk wani mai hannu a ciki.
Daga nan mage ta daina barci, wata rana Allah Ya tarfa wa garinta nono ta cafke bera.
Washegari ta gabatar da jawabinta wurin sarki, sarki ya sa aka taho da bera. Bayan an gudanar da bincike ne aka gano bera na ba budurwarsa kayayyakin da yake sacewa ne.
Aka yi musu bulala, sannan aka kore ta daga aiki. Sarki ya ce tun da mage ta yi sakaci da aikinta har aka shiga taskarsa, sai ya sallame ta a aiki.
Wannan ya bakanta ran mage, ta rika farautar bera har wata rana ta samu sa’a ta kama shi. Bayan ta kashe shi ne ta cinye shi.
Hakan ne ya sa tun daga wannan lokacin mage take kashe bera ta cinye.