Barka da warhaka Manyan Gobe 10

Ina fata kun kammala jarrabawa lafiya. Ina muku addu’ar Allah Ya sa ku samu sakamako mai kyau, amin. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da Karen daji. Labarin na kunshe da alfanun jin maganar na gaba.  A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin Tunkiya da Karen daji Akwai wani makiyayi da yake zuwa […]

Barka da warhaka Manyan Gobe 10

Ina fata kun kammala jarrabawa lafiya. Ina muku addu’ar Allah Ya sa ku samu sakamako mai kyau, amin. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da Karen daji. Labarin na kunshe da alfanun jin maganar na gaba.  A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Labarin Tunkiya da Karen daji

Akwai wani makiyayi da yake zuwa kiwo da tumakansa cikin daji. A cikin tumakansa akwai wata tunkiya da idan sun fita kiwo kullum, sai ta rika mamakin dalilin da ya sa makiyayinsu ba ya son su ketare wani fili. Ita kuwa tana ganin cewa harawar da ke nesa za ta fi dadi tun da ba a zuwa wajen don yin kiwo.
Sai rannan ta faki idon ‘yan uwanta da makiyayi ta je inda aka hana su zuwa kiwo. Isarta wurin ke da wuya sai ta hadu da karen daji. Ya ce da ita ya samu abinci, sai tunkiya ta tsorata. Can sai ta ga inuwar zomo, sai ta kira zomo da ya zo ya taimaka mata.
Jin hakan sai ya ba karen daji dariya. Ya ce, ai zomo karamin alhaki ne domin zai iya kashe shi. Sai zomo ya ce ya yi gaskiya. Amma bari ya duba masa ko babu mafarauta a kusa da za su kashe shi. Sai karen daji ya ce yana jiransa ya je ya dawo.
Da zomo ya bar wurin sai ya samu takarda da alkalami a kasa sai ya yi rubutu ya ninke. Karen daji na ganinsa sai ya ce ka hadu da su? Ya ce bai ga kowa ba amma ya yi tsintuwar wasika. Karen daji ya ce ya karanta masa saboda shi bai iya karatu ba.
Zomo ya ce sako ne daga fadar sarki. Akan cewa ana neman  fatar karen daji domin yi wa sarki riguna. A yanzu an samu 74 saura daya ake bukata. Jin hakan sai karen daji ya ruga a guje don ya tsira da ransa, sai tunkiya ta gode wa zomo. Zomo kuma ya ce mata kada ta sake zuwa inda aka hana ta.