Barka da warhaka Manyan Gobe 12
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku ci gaban labarin Azzalumin Sarki. Labarin na kunshe da darasin cewa zulunci ba ya kara wa mutum komai. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin Azzalumin Sarki (2) Bayan yaro kammala tsinko wa sarki ’ya’yan kuka, sai ya […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku ci gaban labarin Azzalumin Sarki. Labarin na kunshe da darasin cewa zulunci ba ya kara wa mutum komai.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin Azzalumin Sarki (2)
Bayan yaro kammala tsinko wa sarki ’ya’yan kuka, sai ya duba bai ga tsani ba. Ya kokarta dai ya sauko. Bayan ya fara tafiya sai ya hadu da namun daji, inda suka rika bin sa don su kashe shi. Ya rika gudu har ya tsira ya koma gida.
Washegari, yaro ya sake koma wa wajen Sarki. Sarki na ganinsa sai ransa ya baci. Ya ce ya kawo wa sarki ’ya’yan kukar da ya sanya ya tsinko masa ne. Sai ya sanya dogarai suka daure shi a jikin bishiya a tsakar gidan Sarki. Ya kwashe iyalansa don su bar gari. Domin ya sanya a kashe iyayen yaron don ya gaje dukiyar mahaifinsa. Ya yi tafiyar ne domin kada a zarge shi. Yaro ya ga wani dutse ya boye a jakarsa.
Can a kan hanyarsu sai matar sarki ta ce ta yi mantuwa. Ta manta da dutsenta sai ta koma gida ta dauko. Yaro ya yi kamar bai gan ta ba. Tana ta bincike. Daga baya dai ya tambaye ta me take nema? Ta ce dutse. Ya ce idan ta kunce shi zai ba ta. Tana kunce shi sai ya daure ta. Ya sanya mata kayansa, shi kuwa ya sauya shigarsa irin ta matar Sarki.
Yaro ya koma ya tarar da su Sarki, sannan suka ci gaba da tafiya. A hanyarsu sai suka hadu da wasu miyagun mutane. Suka yake su, sai yaro ya cire dankwalinsa. Sarki kuma ya riga ya sa a kashe yaro. Ran Sarki ya baci. Sai kokuwa ta barke tsakaninsa da yaro. Yaro ya ci nasara ya kashe Sarki. Da ya dawo gida, sai ya kwashe iyayensa suka bar garin.
To Manyan Gobe, kowa ya gina ramin mugunta, shi zai fada ciki.