Barka da warhaka Manyan Gobe 15

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Malama da zobenta. Labarin na kunshe da yadda cin zali ke haifar da bacin rai. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin Malama da zobenta A wata makaranta ce aka yi wata malama da ta mallaki zoben zinari. Maigidanta ne ya ba ta […]

Barka da warhaka Manyan Gobe 15
Barka da warhaka Manyan Gobe 15

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Malama da zobenta. Labarin na kunshe da yadda cin zali ke haifar da bacin rai.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Malama da zobenta

A wata makaranta ce aka yi wata malama da ta mallaki zoben zinari. Maigidanta ne ya ba ta a ranar aurensu. Rannan da ta kalli yatsanta sai ba ta ga zoben zinarin ba, sai ta shiga cikin damuwa.
Washegari ta shiga aji domin ta koyar kamar yadda ta saba, sai dalibai suka gaishe ta, amma abin mamaki ba ta ma san sun yi hakan ba, sai daya daga cikin dalibanta ya tambaye ta, “Malama lafiya mun gaishe ki amma ba ki amsa mana ba?” A nan ne ta gaya musu halin da take ciki. Kuma ta yi wa duk wanda ya gano mata zoben alkawarin naira ashirin.
Can sai aka kada kararrawar farko. Yara suka shiga neman zobe amma ban da Salim. daya daga cikin daliban Zubairu ya tambayi Salim ko zai shiga neman zoben, Salim ya ce “Allah Ya kiyaye ni wasa zan yi.”
Zubairu da sauran yaran suka dage da neman zobe. Can sai Zubairu ya yi ihu ya ce “Na samu zobe!” Salim ya ce ya ba shi, amma Zubairu ya ki. Daga nan Zubairu ya kai masa naushi. Don zafin naushin sai Zubairu ya ba shi zoben. Salim na tsoron kada a gano shi, sai ya mayar wa Zubairu zoben ya ce da shi, idan an ba shi naira ashirin din ya ba shi sha biyar, sannan Zubairu ya dau biyar.
Da aka dawo aji, Zubairu ya ba  malamar zobenta, kuma ya ba ta labarin yadda suka yi da Salim, sai malamar tasa aka ba Zubairu naira ashirin kuma aka yi wa Salim bulala goma sha biyar.