Barka da warhaka Manyan Gobe 16
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Musa mai a daidaita sahu. Labarin ya kunshi yadda Musa ya kyautata wa wasu ‘yan jami’a har a karshe suka saka masa da alheri. A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi. Labarin Musa mai a daidaita sahu Wata rana a wani gari da ake […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin Musa mai a daidaita sahu. Labarin ya kunshi yadda Musa ya kyautata wa wasu ‘yan jami’a har a karshe suka saka masa da alheri.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi.
Labarin Musa mai a daidaita sahu
Wata rana a wani gari da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, ko ina ya jike. Saboda ruwan saman da aka yi sai garin ya yi sanyi sosai. Akwai wasu ‘yan jami’a da suke ta hira a jami’a, bayan sun duba agogonsu ne sai suka ga ashe dare ya yi, ga shi suna son komawa gida. Sai suka fita neman a daidaita sahu, duk wadanda suka daga wa hannu sai su ki tsayawa, sai Musa. Sai suka roke shi ya kai su wurin da za su sayi shayi. Da suka isa wurin, sai suka nemi ya zo su sha shayi, amma ya ce musu ya koshi. Har abin ya ba daya daga cikinsu haushi.
Da suka gama shan shayin, sai suka ce masa ya kai su gida. Bayan sun isa gidan ne, sai suka ga Musa bai ce su ba shi kudi mai yawa ba.
Abin ya ba su mamaki, sai daya daga cikinsu ya ce, don Allah ya gaya musu dalilin da ya sa ya ki shan shayi. Musa ya ce ai mai dakinsa ce ta haihu kuma yana kokarin neman kudin suna. Jin hakan sai suka tausaya masa, suka hada masa kudi mai yawa. Amma Musa ya ki karba. Da kyar suka ci nasara ya karba. Musa ya gode musu. Ya ce ai kudin da suka ba shi ma ya ishe shi ya sayi kayan suna.