Barka da warhaka Manyan Gobe 18
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na taho muku da guzurin labarin Kamilu da wata tsohuwa. Sai ku bi labarin sau da kafa don karuwa da darussan da labarin yake koyarwa.A sha karatu lafiya Naku Bashir Musa Liman Labarin Kamilu da Tsohuwa A wani lokaci da ya wuce an yi wani yaro […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na taho muku da guzurin labarin Kamilu da wata tsohuwa. Sai ku bi labarin sau da kafa don karuwa da darussan da labarin yake koyarwa.
A sha karatu lafiya Naku Bashir Musa Liman
Labarin Kamilu da Tsohuwa
A wani lokaci da ya wuce an yi wani yaro da ake kira Kamilu. Yaro ne mai ladabi da biyayya. Yana girmama na gaba da shi, sannan ba ya raina na kasa da shi. Kowa yana yabonsa saboda kirkinsa. Ba ya neman tsokana ballantana ya yi fada. Yana da hakuri tamkar damo da ake yi wa kirarin sarkin hakuri.
Ana cikin haka ne wata rana ya je gona sai hadari ya taso, hakan ya sanya ya kama hanyar dawowa gida, yana tafiya ne ya hadu da wata tsohuwa dauke da wani kwando niki-niki tana tafiya da kyar kamar za ta fadi.
Cikin sauri ya karbi tsohuwar bayan ya karasa wurinta. Daga nan suka ci gaba da tafiya, inda aka fara yayyafi. Haka suka ci gaba da tafiya har ya kai mata gidanta, sannan ya hura mata wuta saboda ruwan da ya taba su lokacin suke kan hanya.
Tsohuwar ta ji dadi har sai ta ba shi kyautar Naira hamsin, amma ya ki karba, ya ce mata ya yi ne don Allah.
Daga nan ta yi masa addu’a: “Allah Ya saka maka da alheri. Ya raba ka da sharrin da ke cikin duniya.” Ya amsa, sannan ya fita.
Sanarwa:
Manyan Gobe za su iya aiko da hotunansu ta adireshi kamar haka: [email protected]