Barka da warhaka Manyan Gobe 19
Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku amsar labarin Gizo-gizo da Kyankyaso da kuma Fara. Ina fata za ku bi bayanin bi-da-bi.A sha karatu lafiya Amsar labarin Gizo-gizo da Kyankyanso da Fara A wani kauye mai yalwar bishiyoyi akwai wani uba da dansa da ke hira, yana ba […]
Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku amsar labarin Gizo-gizo da Kyankyaso da kuma Fara. Ina fata za ku bi bayanin bi-da-bi.
A sha karatu lafiya
Amsar labarin Gizo-gizo da Kyankyanso da Fara
A wani kauye mai yalwar bishiyoyi akwai wani uba da dansa da ke hira, yana ba dansa labarin gizo-gizo da kyankyaso da kuma fara, ya ce masa: “Gizo-gizo na da kafafu 8, kyankyaso kuma na da kafafu 6 da fuka-fukai 4, inda fara take da kafafu 6 da fuka-fukai 2, sai aka zuba wadannan kwari 18 a cikin keji ba tare da ka gani ba, amma jumullar kafafunsu 118, yawan fuka-fukansu kuma 40, don haka a yanzu ina so ka fada mini yawan gizo-gizo da kyankyaso da kuma farar da ke cikin kejin.”
Amsar labarin
Muna da gizo-gizo 5 da kyankyaso 7 da kuma fara 6. Idan ka hada 5+7+6= 18. Gizo-gizo na da kafafu 8, kyankyaso na da kafa 6 da fuka-fukai 4, fara na da kafafu 6 da fuka-fukai 2. Don haka 5(8)+6(7)+6(6)= 118, wato 40+42+36= za a samu kafafu 118.
Ga batun fuka-fukai kuma: 7(4)+6(2)= 28+12=40, an samu fuka-fuki 40.