Barka da warhaka Manyan Gobe 2
Yaya karatu? Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “zomo da kunkuru”. Labarin na kunshe da yadda kunkuru ya samu nasara a kan zomo. A sha karatu lafiya.Taku:Gwaggo Amina Abdullahi Labarin kunkuru da zomo An yi wani zomo a wani daji da ke ji da kansa, yana alfaharin ya […]
Yaya karatu? Da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “zomo da kunkuru”. Labarin na kunshe da yadda kunkuru ya samu nasara a kan zomo.
A sha karatu lafiya.
Taku:Gwaggo Amina Abdullahi
Labarin kunkuru da zomo
An yi wani zomo a wani daji da ke ji da kansa, yana alfaharin ya fi kowace halitta iya gudu. Ana cikin haka sai labarin ya isa kunnen kunkuru.
Sai kunkuru ya kira zomo ya ce masa yana son su yi gasar tsere. Abin sai ya ba zomo da sauran namun daji dariya da kuma mamaki. Suka rika mamakin yadda kunkuru zai wuce zomo yayin gasar.
Can sai aka fara gasar, amma saboda raini sai zomo ya ce ya gaji bari ya kwanta ya danyi barci, dalilinsa kunkuru ba shi da saurin tafiya ballantana gudu.
Kunkuru kuwa sai ya dage yana ta tafiya ba tare da hutawa ba har ya isa layin karshe. Ganin hakan, sai sauran namun daji suka fara ihu. Ihunsu ne ya tayar da zomo. Can sai ya fara hada hannuwansa da kafafunsa domin ya riga kunkuru amma ina bakin alkalami ya bushe.
Sai aka ba kunkuru lambar yabo a kan ya fi zomo gudu.
Manyan Gobe, kwazon kunkuru ne ya sa ya samu nasara a kan zomo, saboda haka ina son ku zama masu kokari da hazaka wurin karatu. Ganin wane ya saba daukar na daya a aji ba shi zai hana ku dagewa ba, domin idan kuka yi kokari za ku cim ma burinku.