Barka da warhaka Manyan Gobe 20
Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin Faisal da malaminsa. Labarin yana dauke da darasin a rika bin rayuwa a hankali, a daina gaggawa, domin gaggawa tana daga shaidan, tana kuma jawo da-na-sani. Ina fata za ku bi labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa..A sha […]
Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin Faisal da malaminsa. Labarin yana dauke da darasin a rika bin rayuwa a hankali, a daina gaggawa, domin gaggawa tana daga shaidan, tana kuma jawo da-na-sani. Ina fata za ku bi labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa..
A sha karatu lafiya
Naku Bashir Musa Liman
Labarin Faisal da Malaminsa
Wata rana wani malami yana tafiya zuwa gonar makarantar da yake koyarwa, sai ya ji ihun neman agaji bayan ya karaso kududdufin da ke kusa da gonar makarantar. Cikin sauri ya kalli wurin da ya ji ihun. Bayan ya kalli cikin kududdufin ne sai ya hango dalibinsa Faisal ne yake ihun neman agaji saboda ruwa na kokarin tafiya da shi.
Da Faisal ya ga malaminsa, sai ya fara ihun malamin ya taimaka masa, Malamin ya ce ya kwantar da hankalinsa. Ya ce: “Kada ka daga hankalinka, zan fito da kai, amma da yaya ka fada cikin kududdufin bayan ba ka iya ruwa ba?”
“Ina koyon ninkaya da taimakon wani katako ne, bayan wani lokaci sai na ga kamar na koya, sai na fara ninkaya babu katakon, shi ne daga baya igiyar ruwan ta fi karfina.” Faisal ya ba da amsa cikin tashin hankali.
Bayan malamin ya waiga ne sai ya hango wani katako a gefensa, cikin sauri ya wurga masa. Bayan ya kama katakon ne ya fara ninkaya har ya fito gabar kududdufin. Bayan ya fito sai ya yi wa malamin godiya. A nan ya yi masa fada, ya ce masa kada ya rika yin gaggawa a rayuwarsa, ya rika bin komai mataki-mataki.
Sanarwa
Manyan Gobe za ku iya turo da hotunanku zuwa wadannan adireshin imel: [email protected] ko [email protected]
Ku rika sanya cikakken sunanku kafin ku turo da hotunan.