Barka da warhaka Manyan Gobe 22
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin wani Malami da kuma bera. Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don cin ribar darussan da ke cikinsa.A sha karatu lafiya Labarin Malami da bera A wani lokaci da ya shude akwai wani malami da ke zaune a bayan […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin wani Malami da kuma bera. Ina fata za ku bi labarin sau da kafa don cin ribar darussan da ke cikinsa.
A sha karatu lafiya
Labarin Malami da bera
A wani lokaci da ya shude akwai wani malami da ke zaune a bayan gari a wani kauye. Malamin talaka ne domin ya dogara a kan sadakar da mutane suke ba shi. Hakan ya sanya bai cika samun sadaka ba, saboda a bayan gari yake zama. Malamin yana da wata ragaya da yake ajiye abincin da aka ba shi sadaka a ciki.
Wata rana abokinsa ya kawo masa ziyara, sai ya ga abokin nasa ya raba hankalinsa, yana ta yi masa hira, amma malamin ya mayar da hankalinsa wajen korar wani bera da sandarsa. Ganin haka sai ya tambaye shi: “Me kake yi ne haka? Me ya sa ka raba hankalinka?”
“Wani bera ne ya sanya ni a gaba, duk abincin da nake ajiyewa a ragayata sai ya je ya lalata ko ya sace. Ina mamakin yadda beran ya samu karfin da yake iya tsalle ya hau ragayata ma. Abin ya ishe ni.” Inji Malamin.
Abokinsa ya ce duk yadda aka yi beran ya tara abinci, abin da za a yi yanzu shi ne, su bincika ko za su samu ramin beran, haka kuwa suka yi, domin bayan sun bincika sai suka gano ramin beran, inda bayan sun duba ramin suka ga abinci mai yawa da ya tara.
Suka kwashe abincin, sannan suka toshe ramin. Hakan ya bakanta wa beran rai, domin ya kwashe lokaci mai tsawo yana wahalar tara abinci, amma ta tashi a banza. Hakan ya sanya ya yi kaura, malamin ya samu lafiya.