Barka da warhaka Manyan Gobe 23
Ina fata kuna cikin qoshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku Labarain Sarki da bawa. Labarin ya qunshi yadda Manyan gobe za su kasance masu taimako a wurin da ake buqatar taimakonsu. A sha karatu lafiya.Naku Bashir Musa Liman Labarin Sarki da Bawa An yi wani azzalumin sarki a wani qauye. Wannan sarkin kullum […]
Ina fata kuna cikin qoshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku Labarain Sarki da bawa. Labarin ya qunshi yadda Manyan gobe za su kasance masu taimako a wurin da ake buqatar taimakonsu.
A sha karatu lafiya.
Naku Bashir Musa Liman
Labarin Sarki da Bawa
An yi wani azzalumin sarki a wani qauye. Wannan sarkin kullum yana quntata wa bayinsa, ga shi ba ya ba su abinci kamar yadda ya kamata. Abin ya ishe su, kuma ba su san yadda za su yi ba.
Rannan sai xaya daga cikin bayin ya gudu daji. Ya shiga cikin kogon zaki. Yana cikin hutawa ke nan sai ya ji wata qara kamar ta zaki. Waigawar da ya yi sai ya ga qaton zaki cikin jini, bayan ya duba ne sai ya ga wani qarfe ya shiga masa qafa.
Nan take ya taimaka wa zakin ta hanyar cire masa qarfen, daga nan suka zama abokai.
Da sarki bai ga bawansa ba sai ya sa aka shiga nemansa, har aka kama shi. Sarki ya ce zai masa mummunan horo saboda ya zama izna ga sauran bayin.
Daga nan sarki ya sa aka tara mutanen qauyensa, sannan aka jefa wannan bawan cikin wani fili da aka zagaye da itatuwa, sai aka sako masa zaki.
Mutanen qauyen suka zuba ido don ganin abin da zai faru, amma ga mamakinsu sai suka ga zaki ya fara lashe bawan sarki. Ashe zakin da bawan ya taimakawa ne. Abin ya ba sarkin mamaki, sai ya haqura da hukuncin kisa da ya yanke wa bawansa, daga qarshe aka sake shi
Da fatan Manyan gobe za su kasance masu taimako, kuma su xauki darasi daga wannan labarin.