Barka da warhaka Manyan Gobe 25

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. Yaya shriye-shiryen koma wa makaranta? A wannan makon na kawo muku labarin ‘kuda da Tururuwa’. Labarin na kunshe da darasin kowa ya fara duba matsalolinsa kafin ya duba na wadansu, wato kada ka rika hawa tudun laifinka kana hango na wadansu. A sha karatu […]

Barka da warhaka Manyan Gobe 25
Barka da warhaka Manyan Gobe 25

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka, amin. Yaya shriye-shiryen koma wa makaranta? A wannan makon na kawo muku labarin ‘kuda da Tururuwa’. Labarin na kunshe da darasin kowa ya fara duba matsalolinsa kafin ya duba na wadansu, wato kada ka rika hawa tudun laifinka kana hango na wadansu.
A sha karatu lafiya
Naku Bashir Musa Liman

Labarin kuda da Tururuwa

A wani lokaci da ya shude an yi wani kuda da ke takaddama da tururuwa kan wanda ya fi yin rayuwar jin dadi.
kuda ya fada wa tururuwa: “Me kika dauki kanki? Ta yaya ma za ki yi gangancin hada kanki da ni? Kalle ni da kyau! Ke kullum kina cikin shan wahala wajen neman abin da za ki ci, amma kullum ina tare da masu kudi da sarakuna, kai idan na ga dama in hau kan sarki da sarauniya, in yi nutso a cikin abincin da za su ci ba tare da na sha wahala ba, ina da damar in shiga ko’ina.” Ya yi shiru, a lokaci guda ya fara dariyar kasaita bayan ya kalli tururuwa.
Tururuwa ta ja dogon numfashi, sannan ta rausayar da kanta, daga bisani ta fara magana: “Kada ka rika dagawa da jiji-da-kai, shin ka tambayi kanka sarakuna da sarauniyoyi da sauran jama’a na kaunarka? Kullum idan sun gan ka a kusa da su sai sun yi bakin ciki, wadansu su kai ma duka, wadansu su nemi maganin da zai halaka ka saboda ka zama musu annoba, idan tsautsayi ya sanya ka mutu a cikin abincinsu wadansu zubarwa suke yi. Idan haka ne mene ne na hura hanci da kafafar kana rayuwar jin dadi?” Ta kalle shi, bai ba ta amsa ba, face jirkicewar da fuskarsa ta yi zuwa bakin ciki.
“Don haka, ka sani kai malalaci ne, ba ka neman na kanka, amma ka lura kullum ina cikin hidimar tara abin da zan ci, idan aka fara ruwa, ko lokacin sanyi da rani, sai in shige cikin dakina in rika cin abincin da na tara.” Ta fada masa, sannan ba tare ta saurare shi ba ta bar shi a wajen, kamar zai yi mata magana sai ya kasa saboda ba shi da abin da zai ce.