Barka da warhaka Manyan Gobe 27
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Azzalumin Sarki. Labarin na kunshe da darasin zulunci ba ya kara wa mutum komai. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin Azzalumin Sarki A wani lokaci akwai wani mutum mai suna Tanko. Allah Ya ba shi dukiya […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Azzalumin Sarki. Labarin na kunshe da darasin zulunci ba ya kara wa mutum komai.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin Azzalumin Sarki
A wani lokaci akwai wani mutum mai suna Tanko. Allah Ya ba shi dukiya mai yawa. Ganin dukiyar da yake da ita sai sarkin yankinsu ya fara tunanin yadda zai mallake dukiyarsa. Rannan sarki ya tura a kira Tanko. Bayan ya zo fada sai ya ce zai yi masa wasu tambayoyi, idan ya amsa su daidai zai bar shi da dukiyarsa, idan bai amsa su daidai ba zai kwace dukiyarsa. Wannan abu ba karamin daga hankalin Tanko ya yi ba. Ya koma gida ya tarar da matarsa mai ciki, sai ya ba ta labarin abin da sarki ya fada masa.
Suna cikin jimamin yadda za su bullowa al’marin yi sai ta ji dan cikinta ya yi magana, ya ce: “Mama ki haife ni,” ta ce yaya za a yi ta haife shi tun lokacinsa bai yi ba. Ya ce ta zaga murhu sau bakwai. Bayan ta zaga ne sai ta haihu. Aka haife shi da jaka.
Washegari ya kama hanya sai gidan sarki, ya ce mahaifinsa ne ya turo shi wajensa. Sai abin ya ba sarki haushi, amma duk da haka ya ce ya dawo gobe.
Washegari yaro ya sake koma wa gidan sarki, inda ya tambaye shi ko an yi sanyi a garinsu kamar yadda ake yi a nan? Yaro ya ce an yi sanyi sosai don sai da ya lullube jikinsa da bargo. Ya ce ya dawo gobe. A washegari ma ya tambaye shi an yi ruwa kamar yadda aka yi a nan? Ya ce an yi. Sarki dai ya rasa yadda zai yi, sai ya ce ya zo ya raka shi wani wuri.
Suka dinga tafiya daga daji zuwa daji yana tambayar yaron ko ya san sunan dajin ya ce eh. Har sai da suka isa wani dajin da yaron bai san sunansa ba. Ya sa aka sanya wa yaro tsani domin ya hau bishiyar kuka ya tsinko masa, yaro na hawa sai Sarki ya sa aka cire masa tsanin aka bar shi a dajin Allah. Laifin dadi karewa! mu hadu a kashi na biyu.