Barka da warhaka Manyan Gobe 3
Tare da fatan alheri kuma an fara hutu. Yau na kawo muku labarin ’karen daji da tunkiya’. Labarin na kunshe ne da yadda wayo da dabara ta kan zama mafita a koda yaushe Asha karatu lafiya.Taku : Gwaggo Amina Abdullahi‘ karen daji da tunkiya’ Akwai wani karen daji mai yawan cinye sauran namun daji. Wata […]
Tare da fatan alheri kuma an fara hutu. Yau na kawo muku labarin ’karen daji da tunkiya’. Labarin na kunshe ne da yadda wayo da dabara ta kan zama mafita a koda yaushe Asha karatu lafiya.
Taku : Gwaggo Amina Abdullahi
‘ karen daji da tunkiya’
Akwai wani karen daji mai yawan cinye sauran namun daji. Wata rana ya fito farauta sai ya hadu da wata tunkiya. Tunkiyar kuma ita kadai ce . Sai karen daji ya ce da ita ta zo. Sai ta yi masa dabara da cewa “ ai na ji an ce duk dajin nan kafi kowa iya busa algaita. Ko ka busa min in ji yadda take?” Jin hakan sai karen daji ya ji dadin yabon da ta yi masa. Nan take sai karen daji ya fitar da algaita ya fara busawa.
Tunkiya ta fara rawa. Tana tunanin ko ’yan uwanta za su ji sautin algaitar su zo su taimaka mata.  Karen daji ya gama sai tunkiya ta rokeshi da ya sake busa mata algaita. Ana cikin hakan sai ga sauran namun daji suka fito.
Suna ganin karen daji sai suka koreshi a hakan tunkiya ta tsira.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a wannan labarin. Ya kamata a zama masu wayo domin wayo kan zama mafita a kodayaushe.