Barka da warhaka manyan gobe (6)
Assalamu alaikum manyan gobe. Da fatan an yi sallah lafiya? Allah Ya maimaita mana amin. A yau na kawo muku labarin ‘Yawan hanzari na janyo nadama’. Labarin na kunshe da yanda hanzari ya sanya Halima ta yi nadama. A sha karatu lafiya.Taku; Amina Abdullahi ‘Yawan hanzari na janyo nadama’ Halima mata ce wacce take da […]
Assalamu alaikum manyan gobe. Da fatan an yi sallah lafiya? Allah Ya maimaita mana amin. A yau na kawo muku labarin ‘Yawan hanzari na janyo nadama’. Labarin na kunshe da yanda hanzari ya sanya Halima ta yi nadama. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi
‘Yawan hanzari na janyo nadama’
Halima mata ce wacce take da kyanwa. A kullum idan za tafi yi aiki ko za ta tafi unguwa, tana barin wa kyanwar ‘yar jaririyar domin ya kula mata da ita.
Kyawan na son jaririyar sosai har ma wata rana Halima za ta dawo ta samu yarta na dariya sakamakon irin wasanni da ya ke yiwa yarta.
Kamar kullum, rannar za ta kasuwa ta ce da kyawan ya lura mata da ‘yarta kafin ta dawo.
Bayan awanni tana dawowa sai ta ga ko ina da jini a dakin da ‘yarta take. Nan take ta yanke hukuncin cewa ai kyawan ne ya kashe mata ‘ya.
Da ta shiga daki sai ta ga kyanwa bakinta jina-jina. Halima ba tare da yin bincike ba sai ta dauko rafkeken sanda ta kwalawa kyanwa har ya mutu.
Tana shiga dayar dakin sai ta ga wani babban maciji a mace kuma ga ‘yarta a gadonta tana wasa. Sai ta saka ihu tana kuka cewa ta kashe kyanwan da ya ceci ‘yarta kuma ta yi matukar nadamar faruwar hakan.
Toh! manyan gobe tare da fatan za’a rika yin bincike kafin a yanke hukunci.