Barka da warhaka Manyan Gobe: Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Tsuntsu mai kai biyu’. Labarin ya kunshi yadda kiyayya ke jawo halaka.
A sha karatu lafiya.Taku: Amina Abdullahi Labarin tsuntsu mai kai biyu Akwai wani tsuntsu mai kai biyu. Kawunan kullum suna cikin fada da juna duk da cewar jikinsu daya ne, kai ka ce ma kishiyoyi ne. Rannan suna cikin tafiya sai dayan kan ya tsinko dan itace mai zaki. Bayan ya fara ci ne sai […]
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin tsuntsu mai kai biyu
Akwai wani tsuntsu mai kai biyu. Kawunan kullum suna cikin fada da juna duk da cewar jikinsu daya ne, kai ka ce ma kishiyoyi ne. Rannan suna cikin tafiya sai dayan kan ya tsinko dan itace mai zaki. Bayan ya fara ci ne sai ya rika yaba dan itacen cewa da dadi sosai.
Jin hakan sai daya kan ya ce ya ba shi don ya dandana ya ji ya dadin yake. Sai daya kan tsuntsun ya ce ba zai ba shi ba. Domin idan ya ci ai cikinsu gaba daya zai yi musu amfani. dayan kan na kallo har ya gama cinyewa.
Rannan dayan kan shi ma ya tsinko wani dan itace har zai fara ci, sai wani tsuntsu ya ce kada ya ci domin idan ya ci za su mutu. Jin hakan, sai dayan ya yi iya kokarinsa ya ga ya hana dan uwansa ci, amma ya ki ji. Ya ce shi ma yana son ya ji dadin dan itacen. Bayan ya kammala ci ne ba da jimawa ba suka mutu.
To Manyan gobe, da wadannan kawunan tsuntsun suna tausayi da kuma son junansu da ba su mutu ba. Don haka babu kyawu a ki dan uwa.