Barka da warhaka Manyan Gobe13
Ina fata kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘illar son kai’. Labarin ya kunshi yadda son kai ya sanya wata zakanya ta yi asarar ‘ya’yanta uku. A sha karatu lafiya.Taku;Gwaggo Amina Abdullahi Illar son kai Akwai wata zakanya mai ‘ya’ya hudu, na farko ana kiransa dan matara, sai Mata rara kumbe, sai Iyara […]
Ina fata kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘illar son kai’. Labarin ya kunshi yadda son kai ya sanya wata zakanya ta yi asarar ‘ya’yanta uku.
A sha karatu lafiya.
Taku;Gwaggo Amina Abdullahi
Illar son kai
Akwai wata zakanya mai ‘ya’ya hudu, na farko ana kiransa dan matara, sai Mata rara kumbe, sai Iyara iye da kuma Kubula hande. Tana son ‘ya’yanta sosai amma ba ta cika damuwa da kubula hande ba. Kullum idan ta kawo musu abinci sai ta yi waka kamar haka: “dan matara mata rarra ka fito matarara kunbe ka fito, iyara iye ka fito kubula hande ka tsaya.” Sai ‘ya’yan nata uku su fito su ci abinci. Idan sun rage sai kubula hande ya fito ya ci ragowar. Kullum haka take yi.
Rannan wani dodo na yawo sai ya ga yadda take kiran ‘ya’yanta har su fito daga rami. Sai ya je ya yi irin wakar da take yi wa ‘ya’yanta. Sai suka ji muryar ba ta yi kama da ta mahaifiyarsu ba sai suka ki fitowa.
Dodo ya je wajen tsuntsu ya ce ya ba shi muryarsa ko ya kashe shi, sai tsuntsu ya ce masa ya sha ruwan siga. Bayan ya sha ruwan siga ne sai muryarsa ta koma kamar ta zakanya.
Ya je ya yi wakar sai suka fito. Yadda suke fitowa haka yake hadiye su. Bayan dodo ya koshi sai ya tafi.
Da yamma sai zakanya ta zo ta yi waka sai ta ji shiru. Sai kubula hande ya ce mata ai dodo ya cinye su. Sai ta ce ya fito ta kashe shi saboda ya ki taimaka wa ‘yan uwansa, shi kuwa ya ki. Ta rasa inda za ta sa kanta, daga baya ta gane babu kyawu a rika nuna bambanci a tsakanin ‘ya’ya.