Barka da warhaka Manyan Gobe2
Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin maharbi da zomo. Labarin na kunshe da yadda yaudara ta janyo mutuwar zomo. A sha karatu lafiya.Taku: Gwaggo Amina Abdullahi Labarin Maharbi da Zomo Akwai wani maharbi wanda duk kauyensu babu wanda ya kai shi iya harbi. […]
Sallama a gare ku Manyan Gobe tare da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin maharbi da zomo. Labarin na kunshe da yadda yaudara ta janyo mutuwar zomo. A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi
Labarin Maharbi da Zomo
Akwai wani maharbi wanda duk kauyensu babu wanda ya kai shi iya harbi. Rannan yunwa ta dame shi sai ya tafi farauta.
Ya hada tarko ko zai samu naman daji ya yi sanwa da shi. Can sai zomo ya fada tarkon maharbi. Zomo ya yi ta kokarin fita amma ya gagara.
A maimakon ya roki maharbi ya taimaka ya bar shi, sai ya ce wa maharbi: “idan ka fitar da ni zan nuna maka inda sauranmu suke kuma za ka samu abin sanwa da yawa”. Jin haka, sai maharbi ya ce: “ashe kai dan yaudara ne saboda haka sai na kashe ka.”Nan take maharbi ya yanka zomo ya kai gida aka dafa masa.
Da fatan Manyan Gobe za su zama masu alkawari ba masu yaudara ba, kuma za su dauki halayya tagari domin samun mafita a kodayaushe.