Barkanmu da warhaka Manyan Gobe
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na yi muku guzurin Labarin zomo da abokansa. Labarin na yi wa Manyan Gobe nasiha a kan kada su dogara a kan abokansu. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin Zomo da abokansa A wani zamani da ya shude an yi wani zomo a wani […]
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na yi muku guzurin Labarin zomo da abokansa. Labarin na yi wa Manyan Gobe nasiha a kan kada su dogara a kan abokansu.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Labarin Zomo da abokansa
A wani zamani da ya shude an yi wani zomo a wani kauye. Yana da abokai masu yawa, hakan ta sanya yake alfahari. Kullum za a gan shi cikin farin ciki. Lokaci zuwa lokaci yakan shirya biki, inda abokansa ke zuwa a sha shagali.
Rannan sai wani karen daji ya fara bin sa yana so ya kashe shi. Sai ya ruga a guje, ya je wajen giwa ya ce: “ Ya abokiyata giwa don Allah ki taimake ni ki kori karen daji domin yana so ya kashe ni”. Giwa ta ce, “gaskiya ina aiki yanzu ka je wajen biri ya taimake ka.”
Ya sake rugawa a guje ya je wajen biri ya ce, “abokina biri ka taimake ni karen daji na yunkurin kashe ni”. Biri ya ce “gaskiya ina taya mahaifiyata aiki ba zan iya ba sai dai ka je wajen rakumi”. Zomo ya je wajen rakumi shi ma rakumin ya ki taimaka masa.
Sai ya nemi wani rami ya buya a can yadda karen dajin bai same shi ba. Can sai ya fito ransa a bace. Ya ce abokansa ba su taimaka masa da komai ba.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin kuma ba za su rika dogara a kan abokai ba.