Barkanmu da warhaka manyan gobe 02
Barkanmu da sake kasancewa da ku manyan gobe tare da fatan kuna ciki koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yadda jimina ta sami dogon wuya’. Labarin ya kunshi yadda mugun hali yake sanya mutum ya rasa wani abu nasa. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Yadda jimina ta zama mai dogon wuya […]
Barkanmu da sake kasancewa da ku manyan gobe tare da fatan kuna ciki koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yadda jimina ta sami dogon wuya’. Labarin ya kunshi yadda mugun hali yake sanya mutum ya rasa wani abu nasa. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Yadda jimina ta zama mai dogon wuya
Akwai wata kada yunwa ta dame ta. Ta zauna a bakin kogi ko za ta ga alamar wucewar kifi amma shiru.
Da jiran ya ishe ta sai ta shiga cikin ruwan ta ga ko za ta yi sa a, ta dade a ruwan amma ba ta sami komai ba. Can ta gaji ta fito bakin kogin. Jikinta ya yi sanyi sosai.
Ba da dadewa ba sai ta hangi jimina da tukunyarta za ta zo diban ruwa. Jimina na isowa sai kada ta ce mata “Don Allah ki taimaka mini wani abu ne ya shige min hakorina ki tayani cire wa”.
Ashe kada dabara ce ta yi wa jimina tana so ta cinye jiminar ne. Ganin yadda kada ta kasance sai jiminar ta tausaya mata. Ta kai kanta cikin bakin kada.
Sai kada ta rufe baki. Jin hakan sai jimina ta fahimci cewa kadar na kokarin cinye ta. Sai ta yi ta kokarin cire kanta daga bakin kada. A lokacin da take jan kanta daga bakin kada sai wuyanta ya fara kara tsayi. Haka tai ta yi har sai da ta cirewa kada hakori daya.
Zafin hakorin da aka cire wa kada ya sa ta saki jimina daga bakinta. Jimina ta rugo a guje sai gida. Ita ko kada na nan jina-jina kuma babu abincin da za ta ci.
Da fatan manyan gobe za su zama na gari.