Barkanmu da warhaka manyan gobe 03
Tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Aisha mai kirki’. Labarin ya kunshi yadda kyawun hali yake kawo alheri. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi. Labarin Aisha mai kirki A wani garin mai suna Shubu an yi matukar rashin abinci wani lokaci.Saboda haka yunwa […]
Tare da fatan alheri kuma da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Aisha mai kirki’. Labarin ya kunshi yadda kyawun hali yake kawo alheri. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
Labarin Aisha mai kirki
A wani garin mai suna Shubu an yi matukar rashin abinci wani lokaci.Saboda haka yunwa ta addabi mutanen garin sosai. Akwai wani mai kudi a garin ya kasance yana taimaka wa mutanen garin da abinci.
Idan ma’aikatan gidan mai kudin suka fito da abinci sai a yi ta dambe a kan abincin.
Aisha ta kasance a cikin masu neman taimako idan kullum ta je karbar abinci ita ce take kasancewa ta karshe domin tana da hakuri. Bayan kowa ya karbi na sa, sai a bata nata ta wuce gida.
Wata rana, bayan ta karbi rabon karshe kamar kullum bayan ta isa gida, za ta dora sanwa ke nan sai ta ga sulalla a cikin hatsinta.
Washe gari sai ta kai wa mai kudin nan sulallan da ta tsinta a cikin rabon hatsinta. Mai kudin ya yi farin ciki sosai game da yadda ta mayar da kudin. Sai ya kara mata wasu sulallan masu yawa ta tafi gida da su.
Yana da kyau manyan gobe su kasance masu gaskiya a ko da yaushe.