Barkanmu da warhaka manyan gobe 04

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan kuna nan lafiya.A yau na kawo muku labarin “Fici da Nanawo” A sha karatu lafiya.Naku:Abubakar AbdulRahman Dodo Fici da Nanawo Fici da Nanawo sunayen gida ne da aka lakaba wa wasu kananan yara ’yan uwan juna, wadanda a mafi yawan lokuta barci ke raba su. Don haka tare […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe 04
Barkanmu da warhaka manyan gobe 04

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan kuna nan lafiya.A yau na kawo muku labarin “Fici da Nanawo” A sha karatu lafiya.Naku:Abubakar AbdulRahman Dodo

Fici da Nanawo

Fici da Nanawo sunayen gida ne da aka lakaba wa wasu kananan yara ’yan uwan juna, wadanda a mafi yawan lokuta barci ke raba su. Don haka tare suke wasa, idan yau an je gidan su Nanawo an yi wasa, wata rana kuma sai a tafi gidan su Fici a yi kiriniya irin ta yarinta.
Fici ta fi zama a gidan Hajiya kakarta, don haka a can akwai abokan wasa, kuma tana yawan lura da duk wani abu da ake yi a gidan. Saboda haka wata rana sai ka ganta tana ta dungurawa wai ita tana sallah; ko ta dauki kayan mutane ta jika a cikin ruwa, wai tana wanki. A wasu lokuta kuwa sai ka ji ta ce, ‘bari ’yata ta yi barci in yi gurguru,’ wai tana kwaikwayon yar mahaifiyarta da ke yin gurguru.
Ita kuwa Nanawo ko zuma ka ba ta da kayan dadi, in har ba ta son su sai kawai ta tada kayar baya ta rika cewa, ‘Ba ma so! Ba ma so!’ Kuma tana da wani abin wasa wai shi Habibi. Don haka da zarar sun hadu da ’yar uwarta Fici sai su yi ta wasa da Habibi, ko dokin roba na Fici. Wanda duk ya kalli wasannin Fici da Nanawo abin zai yi matukar burge shi, wata sa’a kuma sai mutum ya rasa yadda zai shawo kansu in suka rikice.
Wata sa’a sai Fici ta je har gidan su Nanawo ta kwace mata Habibi ko kuma su yi ta ja-in-ja. Idan kuma ta ga dama sai ta ce Nanawo ga Habibinki. Haka dai suke yin wasannin nishadi da kiriniya iyaye da yayyensu na kallo su yi ta dariya. A wasu lokutan kuma a rika yi musu tsawa don kada su dauki wani abu da zai cutar da su, musamman kayan girki ko wukar yanka kayan miya; ko kwalba ko kusa da makamantansu.
Manyan gobe, abin da ya sanya na ba ku labarin Fici da Nanawo shi ne, ya kamata ku fahimci cewa,kannenku suna lura da ku, ku ne madubin rayuwarsu, inda suke sha’awar duk abin da kuka aikata, ba tare da sun yi la’akari da kyawunsa ko rashin kyawunsa ba.
Rayuwar yara dai ta dogara kacokan a kan koyi da na gaba. Don haka wajibi ne gare ku manyan gobe ku rika yin aiki nagari a gida da waje, musamman idan kuna tare da kannenku wadanda shekarunsu ba su wuce biyu zuwa uku ba, wato dai irin su Fici da Nanawo. Domin na tabbata da a gidan su Fici da Nanawo kuke, watakila za mu iya ganewa ko kuna yin bitar litattafanku, domin za su rika dauka suna kwatanta rubutu da karatu. Kai idan ma kuna yin karatun a kullum, na tabbata Nanawo ba za ta ce ba ma so ba. Lallai wajibi ne ga manyan mutane da kananan su rika zuwa da kananan yara wurin sana’arsu suna gani, ta yadda idan sun yi sha’awarta, to za su girma da sanin abin da za su yi don gudanar da harkokin rayuwa.