Barkanmu da warhaka manyan gobe 05
Tare da fatan an gama hutu lafiya kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Hafiz mai cin zali’. Labarin ya kunshi yadda cin zali yake sanya mutum fadawa cikn wani hali. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi ‘Hafiz mai cin zali’ Hafiz ya kasance mai cin zali a makarantarsu., don […]
Tare da fatan an gama hutu lafiya kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Hafiz mai cin zali’. Labarin ya kunshi yadda cin zali yake sanya mutum fadawa cikn wani hali. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
‘Hafiz mai cin zali’
Hafiz ya kasance mai cin zali a makarantarsu., don haka yara da dama suke tsoronsa kuma duk abin da ya fada masu dole su bi shi.
Akwai wata Aisha ita kuma, duk makarantar ba wanda ya kai ta kokari.Ga shi kuma ajinsu daya da Hafiz.
Rannan malaminsu ya ba su aiki su yi a gida, kamar kullum Aisha ta kammala nata ta kawo makaranta washe gari. Da Hafiz ya hango ta sai ya kwace littafinta ya kwafi duk abin da ta rubuta kamin su bai wa malaminsu.
Malam da ya ga aikinsu ya zo daya sai ya kira su ya tambaye su wa ya kwafi na wani. Malam din ya san cewa dai Hafiz ba shi da kokari.
Ba tare da wata wata ba Hafiz ya amsa cewa shi ya yi aikinsa. Ita kuwa Aisha tana tsoro sai ta ce ita ta kwafi na Hafiz. Sai malaminsu ya ba su sabuwar takarda ya ce su sake domin ya gano gaskiyar lamarin.Nan da nan sai Aisha ta gama nata aikin,ta bar Hafiz yana kallon silin.Sai malam ya yi wa Hafiz bulala goma saboda ya yi karya kuma ya kwafi aikin da ba nasa ba. Aka kuma gaya wa iyayensa irin halinsa a makaranta. Su ma suka kara masa wata tsumagiyar.Ita kuwa Aisha aka ba ta kyauta mai yawa.
Da fatan manyan gobe za su zama na gari kuma ba masu satar amsar juna ba.