Barkanmu da warhaka manyan gobe 06
Assalamu alaikum da fatan kuna lafiya, kuma da fatan kuna girmama mutane domin kuwa wulakanci ba shi da kyau,don haka ne ma yau na kawo muku labari mai taken“Girman kai rawanin tsiya.”.A sha karatu lafiya. Taku Amina Abdullahi Girman kai rawanin tsiya Akwai wani mutum mai suna Alhaji Tanko wanda yake zaune a wani kauye […]
Assalamu alaikum da fatan kuna lafiya, kuma da fatan kuna girmama mutane domin kuwa wulakanci ba shi da kyau,don haka ne ma yau na kawo muku labari mai taken“Girman kai rawanin tsiya.”.A sha karatu lafiya.
Taku Amina Abdullahi
Girman kai rawanin tsiya
Akwai wani mutum mai suna Alhaji Tanko wanda yake zaune a wani kauye mai suna Kurtu.Ya kasance shahararren mai kudi a wannan kauyen.Amma ’ya daya kawai yake da ita kyakkyawa mai suna Larai.Ta kasance mai ji da kanta saboda wannan baiwa da Allah ya yi mata.
Wannan yariya ta taso cikin jin dadi har ta isa aure.Duk wanda ya zo neman aurenta sai ta wulakanta shi ta ce ya yi mata muni kuma talaka ne.Mutane da yawa suna ta zuwa domin labarin kyawunta ya kai ko ina, amma duk wanda ya zo sai ta wulakanta shi ta ce bai yi mata ba.
Ana nan wata rana sai wani kyakkyawan mutum mai kudi ya zo wurinta ya ce sunansa Durumi kuma sunan garinsu kirkir. Sai ta ce “na sami mijin aure”.Iyayenta suka ce ta bari a yi bincike domin su ba su taba jin sunan wannan gari ba amma ta ki , ta ce a yi sauri a daura aure domin kada ta rasa wannan mutum.shi ke nan aka daura aure da wannan mutum ya tafi da ita.Ashe ba mutum ba ne,wani katon kumurci ne,sai ya kai ta wini katon rami na macizai, suka yi ta harbinta tana ta kuka.Sai ta ce ta fasa wannan aure ya kai ta gida,amma ya ce ai kin zama matata.Ke ce mai wulakanta mutane saboda kina da kyau kuma mahaifinki mai kudi ne.Bayan sun yi mata jina-jina da harbi sai suka jeho ta bakin rami tamkar matacciya.Sai wani maharbi ya tsince ta ya kai ta gidan Maigari aka nemo iyayenta.Ganin wannan yarinya a ciki wannan hali ya yi matukar daga hankalin mahaifanta.
Sai suka dukufa wajen neman magani har ta warke.Sai fuskarta ta baci ta yi muni saboda harbin macizan nan, duk lokacin da ta kalli fuskarta a madubi sai ta yi ta kuka.Kuma duk wanda ya zo neman aurenta idan ya ji labari kumurci ya aure ta,ba zai kara dawo wa ba.Haka Larai ta zauna cikin bakin ciki da takaici sakamakon girman kai da wulakanta mutane.
Sanarwa:
Manyan Gobe za su iya aiko da hotunansu ta adireshi kamar haka:
[email protected]