Barkanmu da warhaka manyan gobe 07

Tare da fatan alheri. Yau na kawo muku labarin ’Karen daji da tunkiya’. Labarin na kunshe ne da yadda wayo da dabara kan taimaka a mafi yawan lokuta. Taku : Amina Abdullahi ‘ Karen daji da tunkiya’ Akwai wani karen daji mai yawan cinye sauran namun daji. Rannan yafito farauta sai ya hadu da wata […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe 07
Barkanmu da warhaka manyan gobe 07

Tare da fatan alheri. Yau na kawo muku labarin ’Karen daji da tunkiya’. Labarin na kunshe ne da yadda wayo da dabara kan taimaka a mafi yawan lokuta.

Taku : Amina Abdullahi

‘ Karen daji da tunkiya’

Akwai wani karen daji mai yawan cinye sauran namun daji. Rannan yafito farauta sai ya hadu da wata tunkiya. Tunkiyar kuma ita kadai ce . sai karen daji ya ce da ita ta zo. Sai ta yi masa dabara da cewa “ Ai na ji an ce duk dajin nan ka fi kowa iya busa algaita. Ko za ka busa min na ji yadda take?” Jin hakan sai karen daji ya ji dadin yaba masan da ta yi. Nan take sai karen daji ya fitar da algaita ya fara busawa.
Tunkiya ta fara rawa. Tana tunanin ko ‘yan’uwanta za su ji sautin algaitar su zo su taimaka mata. Karen daji ya gama sai tunkiya ta roke shi da ya sake busa mata algaita. Ana cikin hakan sai ga sauran namun daji sun fito.
Suna ganin karen daji sai suka kore shi, tunkiya kuma ta tsira.
Da fatan Manyan Gobe za su dau darasi a wannan labarin. Ya kamata ku zama masu wayo domin neman mafita a koda yaushe.