Barkanmu da warhaka Manyan Gobe 1

Yaya karatu? Ina fata kuna ba da himma wajen karatu. Allah Ya taimaka amin. A yau na kawo muku labarin ‘Illar son kai’. Labarin na kunshe da yadda Bala ya yi asarar kyautar da mahaifinsa zai ba shi sakamakon son kai. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Labarin illar son kai Bala da Bello […]

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe 1
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe 1

Yaya karatu? Ina fata kuna ba da himma wajen karatu. Allah Ya taimaka amin. A yau na kawo muku labarin ‘Illar son kai’. Labarin na kunshe da yadda Bala ya yi asarar kyautar da mahaifinsa zai ba shi sakamakon son kai.

A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Labarin illar son kai

Bala da Bello ‘yan biyu ne. Suna kama da juna sosai. Bala na da son kansa sosai. Idan an ba su abu su raba sai ya debi mai yawa, sannan ya ba Bello kadan. Da yake abin duniya bai damu Bello ba, sai ya karba ba tare da ya ce wani abu ba.
Rannan mahaifinsu ya ce musu yana son ya raba dukiyarsa, amma yana son ya gwada su. Za su yi tafiya mai tsawo kafin rana ta fadi, kuma yanayin tsawon tafiya yanayin yawan dukiyar da za a ba kowane daga cikinsu.
Bello ya fara tafiya a hankali. Amma Bala ya fara gudu saboda yana son ya samu rabo mai yawa. Can sai ya gaji. Da yamma ta yi sai Bello sai ya dawo gida amma Bala bai dawo gida da wuri ba, domin kafafunsa sun yi zafi da kyar yake takawa.
Sai mahaifinsu ya ce Bello za a ba rabo mai tsoka domin ya dawo gida kafin faduwar rana. Abin ya yi wa Bala ciwo.
To, Manyan Gobe ina fata za ku so wa dan uwanku abin da kuke so wa kanku.