Barkanmu da warhaka manyan gobe (12)

Tare da fatan alheri. A yau na kawo muku labarin marainiya. Labarin yana nuna mahimmanci addu’a. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi Labarin wata marainiya Akwai wata marainiya tana gidan marayu. Ga ta ba ta cika kyau ba. Kullum mutane sai su zo su dauki marayu biyar ko goma. A kullum burinta shi ne […]

Barkanmu da warhaka manyan gobe (12)
Barkanmu da warhaka manyan gobe (12)

Tare da fatan alheri. A yau na kawo muku labarin marainiya. Labarin yana nuna mahimmanci addu’a. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi

Labarin wata marainiya

Akwai wata marainiya tana gidan marayu. Ga ta ba ta cika kyau ba. Kullum mutane sai su zo su dauki marayu biyar ko goma. A kullum burinta shi ne ta ga ita ma an dauke ta.
Abin daya ke bata mata rai shi ne, idan aka zo daukan marayun mafi yawan mutanen kyawawan suke dauka.
Rannan sai ta ce za ta sa a addu’arta a kullum idan ta yi sallah. Sai ta fara a addu’a. Tun mutane masu zuwa daukan marayun suna wuce ta har suka fara kallonta suna mata murmushi. Duk da hakan dai ba ta fasa addu’a ba.
Abin har ya kai ga ana zolayarta cewa zai yi wuya ta sami wanda zai dauke ta. Amma duk da jin irin wadannan kalaman bai sa ta karaya da addu’arta ba.
Rannan sai ga wani mai kudi ya zo da babbar mota tare da matarsa. Masu kula marayun sai suka yi ta kai su wajen kyawawan yara amma matar ta ce ba su yi mata ba. Can suka yi ido hudu da marainiyar. Sai ta ce wannan mummunan take so.
Abin yana ta ba mutane mamaki. A hakan ta tafi gidan masu kudi abinta.
Don haka manyan gobe kada su gajiya da addu’a, kuma su yi imanin cewa a duk lokacin da suka yi addu’a, karbabbiya ce.